• 365

    USD/NGN

Wani babban Sarki a Arewa ya rasu

Wani babban Sarki a Arewa ya rasu

– Wani babban Sarki a Arewacin Najeriya ya kwanta dama

– A jiya ne dai aka rasa Sarkin Deba

– Mai martaba Abubakar Waziri ya rasu yana shekara kusan 80

Wani babban Sarki a Arewa ya rasu

Wani babban Sarki a Arewa ya rasu

An yi wani babban rashi a Arewa da ma kasar Najeriya gaba daya inda aka rasa wani babban Sarki daga cikin mayan Sarakunan Yankin a jiya Alhamis 23 ga watan Maris 2017. Wannan Sarki dai ya dade kan karagar mulki.

Sarki Abubakar Waziri na kasar Deba da ke Jihar Gombe ya rasu ne a wani asibiti da ke Garin Abuja. Mai martaba ya shafe shekaru 33 yana mulki a kasar. Allah dai yayi masa cikawa ne yana mai shekaru kusan 80 a Duniya.

KU KARANTA: An yi Jana'izar mutane 22 da mota ta buge

Shugaban karamar hukumar Yamaltu/Deba ya bayyana rasuwar Mai martaba wanda ya mutu ya bar ‘ya ‘ya 27 da mata 2 da kuma jikoki da sauran ‘yan uwa. Sarkin na 36 ya karbi mulki ne a shekarar 1984 inda ya gaji kakan sa. Marigayi mai martaba dai tsohon Soja ne.

A dalilin irin kokari da gwagwarmaya da tsohon shugaba Cif Olusegun Obasanjo yayi a baya an yanke shawarar nada masa wata Sarauta.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Related news

Tsohon babban Hafsan Sojan Najeriya ya ce yin murabus shine mafi alheri ga shugaba Buhari

Tsohon babban Hafsan Sojan Najeriya ya ce yin murabus shine mafi alheri ga shugaba Buhari

Wani na hannun daman Buhari ya yi babban magana kan shugaban kasa; ku karanta
NAIJ.com
Mailfire view pixel