• 385

    USD/NGN

Allah yayi: An shawo kan rikicin PDP

Allah yayi: An shawo kan rikicin PDP

A wani rahoto daga NAIJ.com mun ji cewa Ali Modu Sheriff da Ahmed Makarfi sun saka hannu a wata takarda da ke nuna cewa sun sasanta

Allah yayi: An shawo kan rikicin PDP

Madalla: An shawo kan rikicin PDP

Shugabannin PDP dai sun rattaba hannu a wata takardar lumana da ke nuna cewa sun sasanta wanda hakan na iya kawo karshen rikicin da ya addabi Jam’iyyar na dogon lokaci. Ali Sheirff din da Ahmad Makarfi dai duk kowa na ikirarin cewa shi ne shugaban Jam’iyyar.

Gwamnan Jihar Bayelsa wanda shi aka nada a matsayin wanda zai sasanta bangarorin Jam’iyyar ne yayi wannan kokari. Gwamna Dickson ya tabbatar da cewa kowa ya sa hannu a takardar da tace babu wanda zai kara caccakar wani.

KU KARANTA: Majalisar Dattawa na yi Shugaba Buhari zagon kasa

Allah yayi: An shawo kan rikicin PDP

Ali Modu Sheriff da Ahmed Makarfi sun sasanta

An dai nemi sa hannun kowane bari na Jam’iyyar, inda Bernard Mikko na bangaren Ali Sheriff ya sa hannu sannan kuma Prince Dayo Adeyeye ya sa hannu a madadin bangaren Ahmed Makarfi. Daga yanzu dai ba za a kara jin sukar juna ba daga wani bangare.

A wannan makon kuma wani Dan Majalisa Honarabul Hassan Anthony mai wakiltar Yankin Jihar Benue a karkashin PDP ya tsere daga Jam’iyyar inda ya koma Jam’iyyar APC mai mulki. Hakan dai na karawa APC karfin rinjaye a Majalisar Tarayya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Related news

Kwamitin binciken su Babachir ya fara aiki ba-kama-hannun yaro

Kwamitin binciken su Babachir ya fara aiki ba-kama-hannun yaro

Kwamitin binciken su Babachir ya fara aiki ba-kama-hannun yaro
NAIJ.com
Mailfire view pixel