• 380

    USD/NGN

Don Allah kada ka daga hannun kowa a zaben 2019, sakon Shehu Sani ga Buhari

Don Allah kada ka daga hannun kowa a zaben 2019, sakon Shehu Sani ga Buhari

- Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Kwamared Shehu Sani yace babu wani gwamna a kasar nan da yake da hurumin yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari fada akan yadda yake gudanar da mulki.

- Shehu Sani ya fadi hakanne a karamar hukumar Chikun lokacin da yake ganawa da shugabannin karamar hukumar.

Shehu Sani

Shehu Sani

Sanata Sani yace Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi aikin da wasu da yawa daga cikin gwamnonin kasar nan basuyi ba bayan kuma ya na kokarin ganin cewa a duk lokacin da suke bukatar kudi ya na amincewa da abasu.

“Kuna karban kason kudaden jihohin ku da na Kananan hukumomi duk wata sabo da haka banga dalilin da za’a ce wai Buhari ne ya gaza ba.

KU KARANTA: Jama'ar Inyamurai ta yi wa Buhari kashedi

“Idan ba kwa son Buhari ya rike ko kuma ya kusanci aminansa toh kuma sai ku tarwatsa naku aminan dake zagaye da ku.

“Shehu Sani ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya daga hannun kowa a zaben 2019 ya bari kowa halinsa ta ficceshi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon wasu nan game da Dino Melaye

Related news

Ko a jiki na: Babachir bayan ya gurfana gaban kwamitin bincike

Ko a jiki na: Babachir bayan ya gurfana gaban kwamitin bincike

Ko a jiki na: Babachir bayan ya gurfana gaban kwamitin bincike
NAIJ.com
Mailfire view pixel