• 363

    USD/NGN

Sojin Najeriya ta musanta zargin kashe makiyaya 17 a kudancin Kaduna

Sojin Najeriya ta musanta zargin kashe makiyaya 17 a kudancin Kaduna

Mataimakin Darektan hudda da jama’a na sojin Najeriya Kingsley Umoh ya musanta zargin da wasu kafofin yada labarai suka yi akan su cewa wai sun kashe makiyaya 17 a kudancin jihar Kaduna.

Sojin Najeriya ta musanta zargin kashe makiyaya 17 a kudancin Kaduna

Sojin Najeriya ta musanta zargin kashe wasu makiyaya a kudancin Kaduna

Ya fadi hakan ne a Kaduna inda ya yi bayanin cewa babu gaskiya a zargin.

NAIJ.com ta ruwaito inda Umoh ke cewa gwamnati ta turo su ne domin samar da zaman lafiya a yankin kuma a duk tsawon zamansu sun sami hadin kai da kyakkyawar mu’amula da sarakuna yankin, kungiyar Miyetti Allah da kuma masu fada aji a yankin.

KU KARANTA KUMA: Tsohon Gwamna Ngilari ya gabatar da shedar rashin lafiyar karya

Ya kuma shawarci mutane musamman masu fada aji a yankin da shugaban al’umman da su kwabi mutane akan yada jita-jita domin hakan hakan zai dagula nasarar samar da tsaro da aka samu zuwa yanzu a yankin.

Ya ce a ranakun 19 zuwa 22 na watan Maris din da muke ciki rundunar sojin ta sami nasaran kama wasu ‘yan ta’adda guda 4 sannan sun kashe 2 kuma akwai wasu biyu da suke daure a hannun jami’an tsaro.

Daga karshe ya ce sojojin sun ci gaba da aikin duba gari dare da rana a hanya da kewayen Gidan-Waya-Jagindi da Asso.

KU KARANTA KUMA: Rikicin majalisa da Ibrahim Magu: Fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani

Ga bidiyon minista Amaechi inda yayi jawabi.

Related news

An gurfanar da ma'akacin makaranta saboda satan N340,000

An gurfanar da ma'akacin makaranta saboda satan N340,000

An gurfanar da ma'akacin makaranta saboda satan N340,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel