An gano ma'aikatan gidan yari 2 da suka taimakawa tsohon Gwamna Ngilari ya tsere

An gano ma'aikatan gidan yari 2 da suka taimakawa tsohon Gwamna Ngilari ya tsere

Hukumar dake kula da gidajen yari ta kasa ta ladabtar da jami’anta biyu na gidan yarin Yola dake jihar Adamawa saboda zargin suna da hannu a takaddamar da ta kunno kai sakamakon belin da wata babbar kotu ta baiwa tsohon gwamnan jihar Barrister Bala James Nggilari ranar Litinin da ta gabata.

Gwamna Ngilari

Legit.ng dai ta samu labarin cewa Shugaban hukumar kula da gidajen yari ta jihar Adamawa Peter Tenkwa ya ce an dakatar da jami’i mai kula da gidan yarin DCP Abubakar Abaka kana aka neme shi ya bayyana a shelkwatar hukumar dake Abuja, yayin da John Bukar ke kulle a gidan yarin Yola.

KU KARANTA: An tura wasu yan luwadi gidan yari a Kano

Peter Tenkwa ya ce yanayin da aka fitar da tsohon gwamna Bala James Nggilari kwanaki biyu da suka gabata ya yi kama da almara saboda dabara aka yi anfani da ita na fitar shi ta barauniyar hanya.

Lokacin da Sashen Hausa ya bukaci sanin wace rana tsohon gwamnann ya fita daga gidan yarin, daya daga cikin lauyoyinsa Barrister Obed Wadzani ya kasa fadin ranar.

Wata majiya da ba a tantance ba ta ce tsohon gwamna Ngillari ya ketara zuwa wata kasa makwafciya Jumhuriyar Kamaru.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ga ra'ayin wasu yan Najeria nan game da shugabancin Muhammadu Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel