• 385

    USD/NGN

Babbar magana! Zazzabin Lassa yayi ajalin mutane 8 a Kano

Babbar magana! Zazzabin Lassa yayi ajalin mutane 8 a Kano

Labaran da muke samu yanzu na nuni da cewa mutane 8 sun rasa ransu a karamar hukumar Tudun wada ta jihar Kano sakamakon wata cutar masassara mai zafin gaske da ke kama da cutar Lassa.

Mai maganin Bera

Mai maganin Bera

Ba saraken dake shugabantar yankin Dr. Bashir Muhammad Dankadai shine ya bayyana haka ga jama'a a jiya lokacin da yake bayar da rahoton sa ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II inda yace cutar ta bulla ne a wani kauye da ke cema Taka-Lafiya kimanin sati 3 da ya wuce.

KU KARANTA: Shararren dan siyasa ya ba Buhari umurni

NAIJ.com dai ta samu labarin cewa Ba saraken ya ci gaba da cewa a lokacin da cutar ta bulla yayi kokarin sanar da karamar hukumar inda kuma suka tura jami'ar lafiya zuwa wurin domin tantancewa.

Lokacin da aka tambayi kwamishinan lafiya na jihar Dr. Ibrahim Getso ya tabbatar mana da cewa kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 8 suka mutu sakamakon bullar cutar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli ra'ayin wasu yan Najeriya game da yan siyasar mu

Related news

Dan Najeriya ya gabje Klitschko a wasan damben Duniya

Dan Najeriya ya gabje Klitschko a wasan damben Duniya

Abin alfahari: Dan Najeriya ya zama ‘Dan damben Duniya
NAIJ.com
Mailfire view pixel