Shin ka san wanene ministan Ilimi a Najeriya?

Shin ka san wanene ministan Ilimi a Najeriya?

Bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashe zaben shugaban kasa na shekarar 2015, ya nada wasu jajirtattun mutane kuma amintattu mukamin ministocin gwamnatinsa.

Cikin wadannan ministoci da shugaban kasa ya nada don taimaka masa da gudanar da mulki tare da cika alkawurran daya daukan ma yan Najeriya akwai wani bawan Allah mai suna Adamu Adamu.

KU KARANTA: Jerin ƙasashen da Buhari ya aika rukunin farko na jakadun Najeriya

An haifi malam Adamu Adamu ne a garin Azare na jihar Bauchi, kuma yayi karatu a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, inda ya karanci fannin kididdiga da tsimi.

Legit.ng ta gano Adamu Adamu kwararren marubuci ne daya shahara wajen fashin baki kan al’amuran yau da kullum a jaridar Daily Trust, inda rubuce rubucensa suke fitowa a duk ranar Juma’a.

Adamu Adamu yayi kaurin suna wajen fadin gaskiya komai dacinta dangane da abubuwan da suka shafi Najeriya da ma duniya gaba daya.

Adamu ya taba zama hadimin tsohon shugaban jam’iyyar PDP Cif Solomon Lar a zamanin dayake gwamnan jihar Filato a karkashin jam’iyyar NPP.

A shekarun baya Adamu Adamu yayi aiki tare da shugaban kasa da Muhamamdu Buhari tun a zamanin dayake jagorantar hukumar PTF har zuwa lokacin daya shiga siyasa a shekarar 2003. A shekarar 2007 Adamu Adamu ne wakilin Buhari a yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar a lokacin a jam’iyyar ANPP Isa Yuguda, sanadiyyar haka Isa Yuguda ya lashe zaben.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga wani ministan Buhari dake cewa kullu yana sauraron koken yan Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel