• 380

    USD/NGN

Ka ji dalilin da zai sa a sauke shugaba Buhari

Ka ji dalilin da zai sa a sauke shugaba Buhari

Sanata Femi Okurounmu yace Majalisa fa na iya tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari a dalilin Ibrahim Magu na Hukumar EFCC

Ka ji dalilin da zai sa a sauke shugaba Buhari

A dalilin Magu; Sanatoci na iya tsige Buhari

Kamar yadda muke samun labari a nan NAIJ.com Sanata Okurounmu yace Majalisa na iya tsige shugaban kasa idan ya nemi ya wuce gona da iri. Sanatan yayi wannan magana ne a dalilin rikicin da ake samu a kan Ibrahim Magu na EFCC.

Sanata Okurounmu yake cewa Majalisa tayi na ta a game da maganar Ibrahim Magu wanda shugaban kasa yake nema ya tilasta cewa sai an tabbatar da shi a matsayin shugaban Hukumar EFCC na din-din.

KU KARANTA: Ba mu ja da baya wajen yaki da cin hanci

Ka ji dalilin da zai sa a sauke shugaba Buhari

Magu: Majalisa na iya tsige shugaban kasa

Mun fahimci cewa dai shugaban kasar na kokarin ya kara aikowa Majalisa da sunan Magu wanda an kora sa har sau biyu. Sanatan yace dokar kasa ta ba kowa damar aikin sa kuma aikin shugaban kasa aiko sunan Magu sannan Majalisa ta duba ta gani ko ya dace ko bai dace ba. Sanatan yace har shugaban kasar sai a tunbuke ba wai Magu kawai ba

Yanzu haka dai a bisa dalilin kin tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban EFCC an maka shugaban Majalisar Bukola Saraki da wasu Sanatoci a kotu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Akwai dan siyasan da bai sata a Najeriya

Related news

Yadda fadar shugaban kasa tayi amai ta lashe

Yadda fadar shugaban kasa tayi amai ta lashe

Yadda aka kori wani Dan jarida don yace shugaba Buhari bai da lafiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel