367

USD/NGN

Majalisar Najeriya za ta kai karar NNPC a gaban EFCC

Majalisar Najeriya za ta kai karar NNPC a gaban EFCC

Kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya da ke nazari kan farashin albarkatun man fetir ya yi barazanar shigar da karar jami’an kamfanin mai na NNPC a gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC sakamakon zargin su da hannu a wata badakalar kudaden ketare.

Majalisar Najeriya za ta kai karar NNPC a gaban EFCC

Majalisar Najeriya za ta gurfanar da NNPC a gaban EFCC

Wannan na zuwa ne a yayin da wasu kamfanonin mai suka musanta karban kudaden duk da cewa babban bankin kasar CBN ya ce sun karba kudaden don gudanar da aikin mai a kasar.

Shugaban Kwamitin Raphael Nnanna Igbokwe ya ce, za su yi bincike mai zurfi don gano yadda badakalar ta rufa-rufa ta shafi jami’an NNPC.

KU KARANTA KUMA: Nafisat Abdullahi tayi kwalkwali

NAIJ.com ta tattaro cewa a makon jiya ne hukumar EFCC ta cafke wasu darektocin CBN saboda zargin su da hannu a badakalar bada kudaden na ketare.

Tuni dai kwamitin ya bukaci karamin Ministan Mai na Najeriya Dr, Ibe Kachikwu da Gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele da su bayyana a gabansa a ranar Juma’a mai zuwa don bada cikakkun bayanai kan wannan lamari mai sarkakiya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon jami'an hukumar zabe da aka gurfanar a gaban wata kotun Abuja.

Related news
Ojukwu ya gaskata maganar Buhari na ganawa da mahaifinsa

Ojukwu ya gaskata maganar Buhari na ganawa da mahaifinsa

Ojukwu ya gaskata maganar Buhari na ganawa da mahaifinsa
NAIJ.com
Mailfire view pixel