Najeriya na bukatar Dala biliyan 1.1 don yaki da Sankarau

Najeriya na bukatar Dala biliyan 1.1 don yaki da Sankarau

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ana bukatar dala biliyan 1 da miliyan 100 don yaki da annubar sankarau a jihohi biyar da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

Najeriya na bukatar Dala biliyan 1.1 don yaki da Sankarau a arewacin kasar

Najeriya na bukatar Dala biliyan 1.1 don yaki da Sankarau

Wannan na zuwa ne bayan shugaban majalisar dattawan kasar Sanata Bukola Saraki ya bayyana cewa, a shirye suke su bai wa gwamnati hadin kai don magance annubar.

KU KARANTA KUMA: Labari da Dumi-Dumi: Boko Haram su yi wani sabon bidiyo

NAIJ.com ta ruwaito cewa mukaddashin shugaban hukumar bunkasa ayyukan lafiya a matakin farko ta kasar Dr. Emmanuel Odu ya bayyana cewa, za a yi amfani da kudaden don samar da rigakafin cutar ga mutane miliyan 22 a jihohin Zamfara da Sokkoto da Kebbi da Katsina da Niger, in da jumullar mutane 328 suka rasa rayukansu.

Kawo yanzu dai annubar ta yadu zuwa jihohi 16 na Najeriya, in da aka samu rahoton da ke cewa, kimanin mutane dubu 2 da 524 sun kamu da ita.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Allah Sarki: Wata dattijuwa ta samu waraka daga makanci sanadiyar aikin agajin lafiya na soji

Allah Sarki: Wata dattijuwa ta samu waraka daga makanci sanadiyar aikin agajin lafiya na soji

Dattijuwa ta samu warakar makanta bayan aikin agajin Soji na inganta lafiya a Ribas
NAIJ.com
Mailfire view pixel