• 385

    USD/NGN

Wani Gwamna yayi maganar da ba a ji dadi ba

Wani Gwamna yayi maganar da ba a ji dadi ba

Yanzu haka cutar sankarau na cigaba da yaduwa a Jihohin Arewa inda da dama su ka mutu, sai dai Gwamna Abdulaziz Yari yace mutane suka jawowa kan su

Wani Gwamna yayi maganar da ba a ji dadi ba

Gwamnan Zamfara Yari

Kalaman Gwamnan Jihar Zamfara ba su yi wa Jama’a dadi ba sam inda ya furta cewa zunuban Jama’a ne ya kawo cutar da ake ta fama da ita a Yankin watau sankarau. Mutane da dama yanzu sun yi ca a kan Gwamnan kamar yadda NAIJ.com ke da labari.

Shugaban Gwamnonin kasar yace babu yadda za ayi zinace-zinace su yi yawa a kasa face Ubangiji ya aiko da wata cuta da za ta gagari Jama’a. Yanzu haka dai cutar ta sankarau ba ta da magani a halin yanzu wanda yara ke ta kara mutuwa.

KU KARANTA: Annobar sankarau ta addabi Jama'a

Wani Gwamna yayi maganar da ba a ji dadi ba

Sankarau: Gwamna Yari yace duk laifin Jama’a ne

Wasu dai na ganin cewa Gwamnan ya nuna lallai shugabannin Najeriya ba su shirya jagorantar jama’a ba. Idan har laifi ne ke jawo haka wani yake cewa ai shugabannin sun fi kowa laifi. Kwanan nan ne ma aka zargi Gwamnan da shan kwana da wasu Naira Miliyan 500 na Gwamnati.

Babbar matsalar da ake fuskanta dai ita ce rashin magunguna a kasa, a Duniya ma dai babu maganin irin wannan cuta sosai wanda hakan ke nuna cewa akwai babbar matsala.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Masu bautar kasa kuma kenan ana cikin raha

Related news

Shire-shiren bukin auren Nura M. Inuwa yana ci gaba da tayar da kura (Karanta)

Shire-shiren bukin auren Nura M. Inuwa yana ci gaba da tayar da kura (Karanta)

Dandalin Kannywood: Shahararren mawaki Nura M. Inuwa zai angwance
NAIJ.com
Mailfire view pixel