'Yan majalisar jihar Filato sun tsige mataimakin kakakin majalisar

'Yan majalisar jihar Filato sun tsige mataimakin kakakin majalisar

- Majalisar dokokin jihar Filato ta tsige mataimakin shugaban majalisar bayan ‘yan majalisar 18 daga cikin 24 sun amince da aka

- ‘Yan majalisar kuma sun amince da Sale Yipmong a matsayin sabuwar mataimakin kakakin majalisar

'Yan majalisar jihar Filato sun tsige mataimakin kakakin majalisar

'Yan majalisar jihar Filato sun amince da Sale Yipmong a matsayin sabuwar mataimakin kakakin majalisar bayan tsige mataimakin kakakin majalisar.

Majalisar dokokin jihar Filato a ranar Laraba, 5 ga watan Afrilu ta tsige mataimakin shugaban majalisar, Yusuf Gagdi ta kuri'u murya.

Gagdi, wanda ya ke wakiltar mazabar Kantana na karamal hukumar Kanam, an zabe shine a karkashin jam’iyyar masu adawa, PDP, amma kwanan nan ya yi sheka zuwa jam’iyyar mai mulki, APC don kauce wa tsigewar ‘yan jam’iyyar masu rinjaye APC, jaridar NAIJ.COM

KU KARANTA KUMA: Tsohuwar ministar Jonathan ta shiga ruwan zafi

Bayan tsigewar, Sale Yipmong mai wakiltar mazabar Dengi ne majalisar ta sanar a matsayin wanda zai gaje shi.

Mambobi 18 daga cikin 24 ne suka rattaba hannu kan daftarin aiki na tsige tsohon shugaban.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali yanda mutane ke tofa albarkacin bakinsu kan ko ya kamata a tarwatsa majalisar dattijai Najeriya

Source: Hausa.naij.com

Related news
Mun amince da shugabancin shugaba Buhari dari bisa dari

Mun amince da shugabancin shugaba Buhari dari bisa dari

Mun amince da shugabancin shugaba Buhari dari bisa dari
NAIJ.com
Mailfire view pixel