Amurka ta kai harin makami mai linzami Syria

Amurka ta kai harin makami mai linzami Syria

Amurka ta yi gaban kan ta wajen kaddamar da hare hare da makamai masu linzami a tashar jiragen saman Syria bayan harin makami mai guba da aka samu a kasar wanda ya hallaka mutane 86.

Amurka ta kai harin makami mai linzami Syria
Amurka ta kai harin makami mai linzami Syria

Shugaban kasar Amurka Donald Trump da ke jawabi kan harin, ya ce sun kaddamar da shi ne a matsayin aikewa da wani sako ga shugaba Bashar Al Assad da kuma kare matsayin kasar su.

KU KARANTA KUMA: Ali Modu Sherrif ya fita a fusace yayinda ake ganawa da JonathanAli Modu Sherrif ya fita a fusace yayinda ake ganawa da Jonathan

Trump ya bukaci hadin kan kawayen Amurka wajen daukar matakan da suka dace dan kawo karshen irin wannan kazamin hari da ke ritsawa da fararen hula.

Amurka ta kai harin makami mai linzami Syria
Shugaban kasar Amurka Trump ya bukaci hadin kan kawayen Amurka wajen daukar matakan da suka dace

Fadar shugaban ta sanar da cewar an kai hari da makamai masu linzamin har sau 59 a tashar jiragen Shayrat inda Amurka ta ce anyi amfani da shi wajen kai harin ranar talata.

Amurka ta kai harin makami mai linzami Syria
Amurka ta kai hari kasar Syria

Bayanai sun ce Amurka ta kai harin ne daga jiragen ruwan yakin ta da ake kira USS Ross da USS Porter da ke tekun Baharrum.

Amurka ta kai harin makami mai linzami Syria
Amurka ta kai harin makami mai linzami Syria

Legit.ng ta tattaro cewa wannan na zuwa ne bayan kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a karo na biyu ya kasa amincewa da shirin gudanar da bincike kan harin makami mai guban da ya kashe mutane 86, ciki harda yara 27.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon Baturiyar dake kawata jihar Lagas.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel