Farfesa Ango Abdullahi ya mayar da martani ga Sarkin Kano

Farfesa Ango Abdullahi ya mayar da martani ga Sarkin Kano

- Farfesa Ango Abdullahi yayi raddi ga batun Sarkin Kano na cewa babu cigaba a Arewa

- Ango Abdullahi yace Arewa sai tafi kowanne yanki samun cigaba idan aka raba Najeriya

Da alamu dai har yanzu kura bata lafa ba biyo bayan zancen da sarkin Kano Muhammadu Sunusi II yayi akan yankin Arewa, inda aka jiyo Farfesa Ango Abdullahi yana mayar masa da martani na ilimi.

Farfesa Ango Abdullahi ya mayar da martani ga Sarkin Kano
Farfesa Ango Abdullahi

Legit.ng ta kawo muku rahoton batun da Sarki Sunusi yayi a yayin taron masu zuba hannun jari daya gudana a jihar Kaduna wanda gwamnatin jihar karkashin jagorancin Malam Nasiru El-Rufai ta shirya, inda aka jiyo Sarkin yana fadin idan da za’a raba Najeriya, toh tabbasa yankin Arewa ce zata fi zamowa koma baya a cikin sauran yankunan kasar.

KU KARANTA: Rashin cigaba a Arewa: ‘Mun gaji da surutu, mafita muke nema’ – Shehu Sani

Sai dai wannan batu bai yi ma shahararren Farfesan nan ba, kuma dattijon Arewa, Ango Abdullahi, inda a wata hira da yayi da jarida Sunday Sun ya bayyana cewar Arewa ce ta yi sanadiyyar cigaba Najeriya a baya kafin samun kudin mai, kuma ko a yanzu zata iya ciyarda kanta gaba.

Ango yace: “Zancen da Sarki yayi baya kan layi, kuma bai san hakikanin alkalumman da suka danganci Arewa ba. Na dade ina bayyana ma duniya cewar Arewa tafi sauran yankunan kasar nan saboda yawan jama’a ga yawan kasa da Allah ya azurtamu da shi, abin nufi shine Arewa ta farka daga barcin da take yi, ta haka ne zamu samu cigaba. Kuma ni ina kira da a raba Najeriya.”

Farfesa Ango Abdullahi ya mayar da martani ga Sarkin Kano
Sarkin Kano

Farfesa Ango Abdullahi ya cigaba fadin: “Kun san Sarkin Kano yaro ne matashi, amma kamata yayi yaje ya karanta tarihin Najeriya, yaje yayi bincike akan abubuwan dake habbaka tattalin arzikin kasa, saboda mu mun san Arewa nada duk abinda ake bukata na cigaban tattalin arziki.”

Daga karshe, Ango Abdullahi yace: “Idan aka ce min anyi rashin shugabanci na gari a Arewa ba zan musa ba, amma ai ba’a Arewa bane kadai. Mun san gaskiya ne ya kamata ace shuwagabannin Arewa sun ciyar da yankin gaba fiye da haka, amam sai suka buge da satar kudaden.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon caccakar da Sarki Muhammadu Sunusi yayi ma shuwagabannin Arewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel