Jama'a na ci gaba da mutuwa ta dalilin cutar sankarau

Jama'a na ci gaba da mutuwa ta dalilin cutar sankarau

- Mutane 438 ne cutar sankarau ta kashe a Najeriya

- Hukumomin Najeriya sun ce kawo yanzu Alkaluman mutane da annobar Sankarau ta kashe a kasar sun kai 438

Cutar sankarau

Cutar sankarau

Jami’in cibiyar da ke hana yaduwar cututtuka ta kasa John Oladejo, da ke tabbatar da haka a rahotan da ya fitar ya ce mamata sun fi yawa a jihar Zamfara.

Yanzu dai ciwon ya yadu zuwa jihohi 19 da ke kasar, yayin da gwamnati ke cewa an kaddamar da rigakafi.

KU KARANTA: Ku kalli kyawawan hotunan wani dan Arewa da ya kware wajen zana motoci

NAIJ.com ta samu labarin cewa a ranar 5 ga watan Afrilu wannan shekarar, mutane 3959 aka tabbatar na dauke da cutar, yayin da 181 aka kebe su.

Rahotanni sun ce mutane na cuncurundo a Zamfara inda cutar tafi yaduwa domin karban rigakafi.

Cutar sankarau na wannan lokaci daban ya ke da wanda aka saba gani a Najeriya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma dai yan Najeriya ne ke tsokaci game da kasafin kudin 2017 na fannin lafiya

Source: Hausa.naij.com

Related news
Biyafara: Ba da mu ba Inji Gwamnan Jihar Benuwe

Biyafara: Ba da mu ba Inji Gwamnan Jihar Benuwe

Fafutukar Biyafara: Ba da mu ba Inji wani Gwamna
NAIJ.com
Mailfire view pixel