Dalilin da yasa Buhari bai halarci taron majalisa na sati ba – Lai Mohammed

Dalilin da yasa Buhari bai halarci taron majalisa na sati ba – Lai Mohammed

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai halarci taron majalisa ba saboda yana gudanar da wasu ayyuka

- A cewar Ministan bayanai, Alhaji Lai Mohammed Buhari bai koma halin rashin lafiya ba

- Ya kuma ce shugaban kasar na nan a gari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai halarci taron majalisa na sati-sati ba, saboda yana gudanar da wasu al’amurori, cewar ministan bayanai, Lai Mohammed.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya jagoranci taron da akayi a fadar shugaban kasa a ranar Laraba, 12 ga watan Afrilu bayan shugaban kasa Buhari yak i hallara.

Rashin bayyanan shugaban kasa ya haifar da cece kuce kan cewa ya kuma fadawa halin rashin lafiya. Kwanakin baya shugaban kasa ya yi kusan kimanin watanni biyu a Landan don hutun ganin likita.

Dalilin da yasa Buhari bai halarci taron majalisa na sati ba – Lai Mohammed

Fadar shugaban kasa ta fadi dalilin da yasa Buhari bai halarci taron majalisa na sati ba

Da yake jawabi ga manema labarai a majalisa a karshen taron, Mr. Mohammed yace, “Shugaban kasa bai fada halin rashin lafiya ba kuma”.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya nada daraktoci 5 a hukumar CBN

Ministan ya kara da cewa “ shugaban kasa na a gari; shugaban kasa na gudanar da wasu al’amura. Ya duba abunda taron ya kunsa sannan ya yanke shawarar cewa mataimakin shugaban kasa yay i jagoranci. Ba sabon abu bane don mataimakin shugaban kasa ya jagoranci taron majalisa.”

A baya NAIJ.com ta ruwaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada manyan daraktocin babban bankin kasar guda biya.

A cewar Femi Adesina, mai ba shugaban kasa shawara na musamman a kafofin watsa labarai da shafukan zumunta, Buhari ya mika sunaye ga masu rinjaye a majalis cikin wata wasika da ya aika ma shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a ranar Laraba, 12 ga watan Afrilu.

Wasikar da ya aika ma shugaban majalisar dattawa na dauke da sunayen wadanda aka zama da yankunan su.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon wani mutumi da yace ya kamata a share majalisar dattawan Najeriya

Source: Hausa.naij.com

Related news
PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2

PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2

PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2
NAIJ.com
Mailfire view pixel