Yan fashin teku sun kashe sojojin Najeriya 2, yayinda suka raunata sojoji 3

Yan fashin teku sun kashe sojojin Najeriya 2, yayinda suka raunata sojoji 3

- Hukumar sojin Najeriya ta rasa sojojinta guda biyu a tekua jihar Rivers

- Sojojin sun mutu ne a yayinda suke mayar da harin da wasu yan fashin teku suka kai a jihar

- Sojojin sun kuma gano tare da lalata matata 13 a yankin Iyalama Adama dake jihar

Hukumar sojin Najeriya tace ta rasa sojojinta guda biyu a ranar Alhamis, 13 ga watan Afrilu.

Legit.ng ta tattaro cewa yan fashi da makamin teku sun kashe sojoji biyu a jihar Rivers bayan sun amsa wani kira mai wahala.

Abubakar Abdullahi, wani kakakin hukumar soji, ne ya tabbatar da afkuwar al’amarin yace: “Rundunar mu sunyi mummunan arangama da yan fashin teku a yayinda yan fashin suka kai hari a yankin Ijawkiri.

Yan fashin teku sun kashe sojojin Najeriya 2, yayinda suka raunata sojoji 3
Hukumar sojojin Najeriya ta rasa jami'anta guda biyu a jihar Rivers

“Abun bakin ciki jaruman sojoji biyu sun rasa rayukansu sun yi babban sadaukarwa a kan aiki, yayinda wasu uku suka ji rauni da harbin bindiga."

Kakakin ya kara da cewa jami’an hadin gwiwa na JTF na nan suna kokarin kama yan ta’addan.

KU KARANTA KUMA: Hukumar EFCC ta kuma babban kamu a jihar Lagas (HOTO)

Yan fashin teku sun kashe sojojin Najeriya 2, yayinda suka raunata sojoji 3
Sojojin sun mutu ne a yayinda suke mayar da harin da wasu yan fashin teku suka kai a jihar

Ya kara da cewa sojojin Operation Delta Safe sun lalata matata uku da basa bisa ka’ida a jihar Rivers.

“A kokarin ta na cimma manufar ta, rundunar Operation Delta Safe dake suntiri a yankin Iyama Adama dake jihar Rivers, a jiya sun gano wasu matata 13 da basa bisa ka’ida sannan kuma sun lalata matatar."

KU KARANTA KUMA: Muna iya fuskantar sabon rikici bayan Boko Haram - Buhari

Ku tuna cewa gwamnatin tarayya tayi alkawarin aiki tare da matata mai da basa bisa ka’ida a yankin Niger Delta.

Osinbajo yace an kafa manufar ne don tallafa ma kokarin gwamnati gurin rage rikice-rikice a Niger Delta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyon na Legit.ng dake nuna yadda hukumar sojin Najeriya ta yaki Boko Haram:

Asali: Legit.ng

Online view pixel