Bayan hari gidanta na Legas, EFCC ta afka gidanta na Abuja

Bayan hari gidanta na Legas, EFCC ta afka gidanta na Abuja

-Hukumar EFCC ta gano makudan kudi gidan tsohuwar ma' akaciyar NNPC a Legas

- Saboda zurfafa bincike, sun sake kai hari gidanta na Abuja

Bayan hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta kai farmaki gidan Mrs. Esther Nnamdi-Ogbue ranan Laraba, 12 ga watan Afrilu a wani gidan tsauni da ke Osborne Towers 16, Osborne road Ikoyi inda suka gano makudan kudi.

Game da cewar jaridar Thisday, kudin $43.4 million, wanda ya kunshi $43.3 million, N23 million da £27,000 jibge a cikin gidan, ba’a san takamammen dalilin da yasa jami’an hukumar suka afka gidanta na Abuja ba.

YANZU-YANZU: bayan gano kudi a gidanta na Legas, hukumar EFCC ta afka gidan Nnamdi Ogbue na Abuja

Makudan kudin

Amma jaridar Thisday ta tuntubi wani dan uwanta, ya karyata cewa ba gidan Mrs. Nnamdi-Ogbue bane aka gano kudin.

KU KARANTA: An kashe barawon mota a jihar Legas

Dan uwan wanda aka sakaye sunansa ya fadawa jaridar Thisdy cewa Mrs. Nnamdi-Ogbue na gida da iyalanta kuma babu wanda ya zo.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2

PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2

PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2
NAIJ.com
Mailfire view pixel