• 385

    USD/NGN

Kudin da hukumar EFCC ta gano $50million na Rotimi Amaechi ne – Femi Fani Kayode

Kudin da hukumar EFCC ta gano $50million na Rotimi Amaechi ne – Femi Fani Kayode

-Tsohon minista ya jingina kudin da aka gano a Legas ga Rotimi Amaechi

- Har yanzu dai Rotimi Amaechi bai futa kalami ba akan al’amarin

Wani tsohon minstan sufurin jirgin sama, Cif Femi Fani Kayode yayi ikirarin cewa kudi $50million da hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gano a jihar Legas na mallakan ministan sufuri ne, Rotimi Amaechi.

Fani Kayode wanda ya bayyana wannan a shafin ra’ayinsa na Tuwita yayi watsi a rahotannin da ke cewa na hukumar leken asiri NIA ce.

Kudin da hukumar EFCC ta gano $50million na Rotimi Amaechi ne – Femi Fani Kayode

Kudin da hukumar EFCC ta gano $50million na Rotimi Amaechi ne – Femi Fani Kayode

Yace: “ kudi $43 million na Rotimi Amaechi ne. kana kuma gidansa ne aka gani kudin. NIA karya takeyi, bata ajiye kudi a gidan minista."

KU KARANTA: Amfanin tafarnuwa ga lafiyan jikin dan Adam

Tsohon shuagban jam’iyyar PDP, Adamu Muazu, yayi amanna da cewa lallai shi ya gina gidan da EFCC ta gano kudin.

Adamu Muazu wanda tsohon gwamnan jihar Bachi ne yace tuni ya sayar da gidan kuma babu ruwansa da wadanda ke zama a ciki yanzu.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Related news

Shugaban NIA da aka dakatar ya sha tambayoyi har na awa 12

Shugaban NIA da aka dakatar ya sha tambayoyi har na awa 12

Kwamitin binciken su Babachir ya fara aiki ba-kama-hannun yaro
NAIJ.com
Mailfire view pixel