PDP zata daukaka kara – Ize Iyamu

PDP zata daukaka kara – Ize Iyamu

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da kuma dan takaranta na gwamna a jihar EDO, Mr Osagie Ize-Iyamu, ya bayyana a garin Benin cewa hukuncin da alkali ya yanke a kotun zabe yau, basu yarda da shi.

Mr Osagie Ize-Iyamu, ya bayyanawa shugabannin jam’iyyar da magoya baya cewa zasu daukaka kara a kotun daukaka kara, kotun Afil.

“Bisa ga abubuwan da naji, wannan hukunci ba zata yiwu a manyan kotuna ba. sai mun kai har kotun koli.”

Hukuncin jihar EDO : PDP zata daukaka kara – Ize Iyamu

Hukuncin jihar EDO : PDP zata daukaka kara – Ize Iyamu

Kotun zabe karkashin jagorancin Justice Ahmed Badamasi a ranan Juma’a yayi watsi da karar da Ize Iyamu ya shigar da jam’iyyar PDP.

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Edo, Cif Dan Orbih, ya gode wa magoya baya kuma yana basu tabbacin cewa abubuwa zasuyi kyau.

KU KARANTA: Ahmed Musa ya saki matarsa saki 3

“Ina son in godewa ubangiji game da abubuwan da muka samu yi zuwa yanzu. Abin farin cikina shine, ubangiji zai bamu gaskiya.

“Kana kuyi kasa a guiwa. Muna sa ran goyon bayanku. Ina kira gareku ku daga tayar da tarzoma.

“Bamu yarda da wannan hukunci ba; ba zamu yarda da shi ba kuma mun fadawa lauyoyin mu su daukaka karan.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Gwamnatin tarayya zata dawo da tsarin Shingen karbar haraji a kan manyan tituna - Ministan Ayyuka

Gwamnatin tarayya zata dawo da tsarin Shingen karbar haraji a kan manyan tituna - Ministan Ayyuka

Gwamnatin tarayya zata dawo da tsarin Shingen karbar haraji a manyan titunan kasa - Ministan Ayyuka
NAIJ.com
Mailfire view pixel