Goodluck Jonathan ya kara shiga cikin wata matsala

Goodluck Jonathan ya kara shiga cikin wata matsala

– Ana zargin tsohon shugaban kasa Jonathan da lashe wasu makudan kudin rijiyoyin man kasar

– Yanzu kuma wata sabuwar badakala ta kara fitowa game da kudin da EFCC ta gano kwanakin baya

– Hukumar NIA ta tsaro ta jefa Jonathan cikin tsaka-mai-wuya

Goodluck Jonathan ya kara shiga cikin wata matsala

Tsohon shugaba Goodluck Jonathan

NAIJ.com ta kawo maku rahoton cewa Kotu ta bada umarni a mikawa Gwamnatin tarayyar Najeriya makudan kudin da Hukumar EFCC ta bankado makon jiya a Ikoyi na Jihar Legas. Wata majiyar tace shugaban kasa ya bada umarni a maidawa bankin kasar kudin.

Bayan an rasa gane wanda ya mallaki kudin har Kotu ta bada umarni a mikawa Gwamnatin tarayyar Najeriya kudin da EFCC ta bankado. Sai dai kuma yanzu ga Hukumar NIA na tsaro tana bayyana cewa kudin ta ne.

KU KARANTA: An gano masu kudin da aka bankado a Legas

Goodluck Jonathan ya kara shiga cikin wata matsala

Shugaba Buhari ya bada umarni a maidawa bankin CBN kudin

Hukumar tace ta tanadi kudin domin gudanar da wasu ayyuka a cikin kasar musamman Garin Legas. Shugaban Hukumar Ayodele Oke ya bayyana cewa tun zamanin shugaba Goodluck Jonathan aka saki wadannan kudi.

Sai dai abin mamaki har yanzu ba a kashe wannan makudan kudi da akwai ta-cewa wajen kasafin su ba. An dai karkatar da makudan kudi ta hanyar tsaro lokacin yakin zaben tsohon shugaba Jonathan Goodluck.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sojojin Najeriya na yaki da Boko Haram

Source: Hausa.naij.com

Related news
Yansanda sun rugurguza matattaran matsafa guda 5 a jihar Legas (Hotuna)

Yansanda sun rugurguza matattaran matsafa guda 5 a jihar Legas (Hotuna)

Yansanda sun rugurguza matattaran matsafa guda 5 a jihar Legas (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel