An jinjinawa gwamnatin tarayya yayinda za’a bude filin jirgin saman Abuja ranan Laraba

An jinjinawa gwamnatin tarayya yayinda za’a bude filin jirgin saman Abuja ranan Laraba

- Za’a bude filin jirgin saman Abuja bayan an makonni 6 da gyara

- Mutane sun yabawa gwamnatin tarayya akan wannan abu da tayi

Kamfanonin jirgin sama, fasinjoji da wasu masu ruwa da tsaki a rana Litinin sun jinjinawa gwamnatin tarayya akan yunkurin da tayi wajen gaggauta kammala aikin gyaran babban filin jirgin saman Nnamdli Azikiwe International Airport (NAIA), da ke Abuja.

Ma’aikatan jirgin saman su alanta cewa za’a cigaba da aiki ciki da wajen Abuja a ranan Laraba, 19 ga watan Afrilu.

Zaku tuna cewa an kulle babban filin jirgin saman Nnamdli Azikiwe International Airport (NAIA), Abuja ranan 8 ga watan Maris kuma an koma amfani da babban filin jirgin saman Kaduna.

Masu ruwa da tsaki sun jinjinawa gwamnatin tarayya yayinda za’a bude filin jirgin saman Abuja ranan Laraba

Masu ruwa da tsaki sun jinjinawa gwamnatin tarayya yayinda za’a bude filin jirgin saman Abuja ranan Laraba

Gwamnatin tarayya tayi alkawarin cewa zata bude filin jirgin saman bayan makonni 6 har ministan sufurin jirgin sama, Sanata Hadi Sirika, yayi alkawarin cewa ajiye aikinsa idan har basu cika alkawarin budewa bayan makonni shidan ba.

Shugaban hukumar jiragen saman Najeriya FAAN, Injiniya. Saleh Dunoma yace za’a kammala aikin kuma hukumar NCAA ta tabbatar da cewa aikin yayi kyau.

KU KARANTA: Ana shigo da shinkafa a boye

Fasinjoji sun jinjinawa gwamnatin tarayya da cika alkawarinsu wajen bude filin jirgin saman a ranan Laraba,19 ga watan Afrilu.

Wani ma’aikacin filin jirgin saman yace : “muna farin ciki gwamnatin tarayya ta cika alkawarinta kuma ba dadewa ba, za’a dawo aiki Abuja.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Kungiyar Hausawa a Ogun ta zargi gwamanatin jihar da rashin damawa da ita

Kungiyar Hausawa a Ogun ta zargi gwamanatin jihar da rashin damawa da ita

Kungiyar Hausawa a Ogun ta zargi gwamanatin jihar da rashin damawa da ita
NAIJ.com
Mailfire view pixel