Shugaba Buhari ya raba shinkafa 136,000 ga ‘yan gudun hijira

Shugaba Buhari ya raba shinkafa 136,000 ga ‘yan gudun hijira

- Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya tallafawa yan gudun hijira da shinkafa 136,000.

- Hukumar kwastam na kasa ta raba wadannan shinkafan bisa umurnin shugaban Buhari ga ‘yan gudun hijiran.

Hukumar kwastan na Najeriya (NCS) ta rarraba buhuna shinkafa 136,476 ga sansanonin ‘yan gudun hijira fadin kasar a cikin shekara daya.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar NCS, Joseph Attah, ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Abuja a ranar Talata, 18 ga watan Afrilu 18. NAIJ.com ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari ta ce za a iya kwashe shekaru kafin a kubutar da ‘yan matan Chibok

Attah ya ce hukumar ta raba wadannan shinkafan ne bisa umurnin shugaban kasa Muhammadu Buhari ga ‘yan gudun hijira.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon farashin kayan abinci a kasuwa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta samar da magungunan yaki da cutar kwalara a sansanin 'yan gudun hijira

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta samar da magungunan yaki da cutar kwalara a sansanin 'yan gudun hijira

An samar da magunguna 915,000 don yaki da cutar kwalara a Borno
NAIJ.com
Mailfire view pixel