Hukumar EFCC ta bada lissafin jimillan kudin da ta kwato ga shugaba Buhari

Hukumar EFCC ta bada lissafin jimillan kudin da ta kwato ga shugaba Buhari

- Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta sallama takardan rahoto kan kudaden da ta kwato a Ikoyi, jihar Legas

- Rahoton ya kunshi bayanai filla-filla akan abinda aka samo a farmakin

Wata rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa hukumar EFCC ta sallama rahoto ga fadar shugaban kasa akan kudi N15 billion da ta gano a wata daki da ke Ikoyi, jihar Legas ranan Laraba, 12 ga watan Afrilu.

Game da cewan rahoton, hukumar yaki da rashawa ta bada rahoton filla-filla akan abubuwan da aka samu da kuma yadda aka samar da kudin.

Hukumar EFCC ta bada lissafin jimillan kudin da ta kwato ga shugaba Buhari

Hukumar EFCC ta bada lissafin jimillan kudin da ta kwato ga shugaba Buhari

Kudin da aka kwato ya kunshi $43.4 million, £27,000 da N23million.

Shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, da ma’aikatansa sun iyakan kokarinsu wajen gano ainihin mamallakan kudin.

KU KARANTA: An hallaka sojin Najeriya 5 a Borno

Hukumar leken asirin tarayya NIA ta ce kudinta ne wanda tsohon shugaba Goodluck Jonathan y ace a bata domin gudanar da ayyukan leken asiri kafin ya sauka daga mulki.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Labarin wani mutumin Arewa da yadda yake neman na abinci a Legas

Labarin wani mutumin Arewa da yadda yake neman na abinci a Legas

Labarin wani mutumin Arewa da yadda yake neman na abinci a Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel