Hukumar NSCDC ta kama dan Boko Haram a jihar Adamawa

Hukumar NSCDC ta kama dan Boko Haram a jihar Adamawa

- An kama wani dan ta’addan Boko Haram da ya fito daga dajin Sambisa a Adamawa

- Dan ta’addan ya ce ya kashe mutane 10 tun da ya shiga kungiyar

Hukumar NSCDC dake Adamawa sun kama wani da ake zargin dan kungiyar Boko Haram, Amos Hassan.

Da yake sanar da manema labarai, shugaban hukumar na jihar, Mista Aliyu Musa, ya fada wa manema labarai cewa an kama Hassan ne a aranar Talata a layin gidajen tarayya (Federal Housing Estate) dake yankin Bajabure na Yola.

"Tawagar mu ne ta kama shi kuma ya bayar da sanarwan cewa ya kashe kimanin mutane 10 tun bayan da ya shiga kungiyar,” cewar Musa.

KU KARANTA KUMA: ‘Wanene fadar shugaban kasa?’ – Babachir Lawal ya maida martani ga dakatar da shi

Ya bayyana cewa dan ta’addan dake dauke da raunukan bindiga ya fito ne daga dajin Sambisa.

Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, Hassan mai shekaru 25 ya ce ya fito ne daga karamar hukumar Azare na jihar Bauchi.

Wanda ake zargin ya ce ya fito ne daga dajin Sambisa.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa kwanaki biyu da suka gabata, yan ta’addan Boko Haram sun kai harin mamaya wani tashar sojoji inda suka kashe sojoji biyar yayinda suka bar wasu biyar da rauni.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Kungiyan Matan Gwamnonin Arewa 19 tayi alkawarin bada gudunmawar ta wajen cigaban kasa

Kungiyan Matan Gwamnonin Arewa 19 tayi alkawarin bada gudunmawar ta wajen cigaban kasa

Kungiyar Matan Gwamnonin Jihohin Arewa 19 ta dau alwashin taimakawa Gwamnatin Tarayya
NAIJ.com
Mailfire view pixel