• 363

    USD/NGN

Boko Haram sun kai wa sojin Najeriya harin bazata

Boko Haram sun kai wa sojin Najeriya harin bazata

- Sama da ‘yan Boko Haram 200 ne suka far ma wata bataliyan sojojin Najeriya sansaninsu a ranar Litinin, 17 ga watan Afrilu

- An rahoto cewa sun kashe sojoji 8 sannan suka raunata wadansu 11 a cikin kwanaki uku

Sama da ‘yan Boko Haram 200 ne suka far ma wata bataliyan sojojin Najeriya a bazata in da suka kashe sojoji 8 sannan suka raunata wadansu 11.

Kamar yadda muka jiyo daga majiyar mu Boko Haram din sun yi wa bataliyan sojin shigar ba za ta ne .

Sojin Najeriya sun yi arangama da Boko Haram din a batakashin da ya dauki kusan awa daya ana gwabzawa.

Boko Haram sun kai wa sojin Najeriya harin bazata

Boko Haram sun kai wa sojin Najeriya harin bazata

Da wuta tayi wuta dai Boko Haram sun koma da baya inda wasunsu suka gudu da raunuka a jikinsu. Sun tafi da makamai da yawa na sojojin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Shugaban NIA, Oke baiyi kuka ba bayan an dakatar da shi – Fadar shugaban kasa

A bayanan da muka samu kuma ya nuna cewa Sojojin Najeriya sun Kashe ‘yan Boko Haram a artabun da akayi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Shin Buhari ya fitar da kasar daga koma bayan tattalin arziki?

Related news

Wata sabuwar cuta mai lalata gonaki ta kuno kai a Jihar Filato

Wata sabuwar cuta mai lalata gonaki ta kuno kai a Jihar Filato

Wata sabuwar cuta mai lalata gonaki ta kuno kai a Jihar Filato
NAIJ.com
Mailfire view pixel