Manchester United ta jajintawa iyalan wadanda suka halaka a gidan kallon kwallo a Calabar

Manchester United ta jajintawa iyalan wadanda suka halaka a gidan kallon kwallo a Calabar

Kungiyar Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta jajintawa iyalan wadanda suka halaka a gidan kallon kwallo a Calabar yayinda suke kallon wasanta da Anderlecht a daren ranan Alhamis.

An samu rahoton cewa Sama da mutane 30 ne suka rasa rayukansu yayinda wayan wuta ya rikito kan kwanon gidan kallon kwallo a garin Calabar, babban birnin jihar Cross River.

Amma daga baya wani dan sanda ya fadawa jaridar Premium Times cewa mutane 7 ne suka hallaka kuma 10 sun jikkata.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta jajintawa iyalan wadanda suka halaka a gidan kallon kwallo a Calabar

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta jajintawa iyalan wadanda suka halaka a gidan kallon kwallo a Calabar

Kungiyar kwallon kafan ta bayyana wannan ne a shafin ra’ayinta na Tuwita inda tace : “ Muna mika sakon ta’aziyarmu ga masoya United, abokansu da iyalansu akan abin takaicin da ya faru a Calabar, kasar Najeriya.”

KU KARANTA: Mutane 30 sun hallaka a gidan kallon kwallo

Wanni wanda ya tsallake rijiya da baya ya bayyanawa jaridar Punch cewa wata transfoma da ke kusa da Iyang-Esu a karamar hukumar Calabar tayi bindiga lokacin da ake wasan wanda ya sabbaba faduwar wayan wuta kan gini gidan kallon kwallon.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Matar tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Sani Abacha tayi shar a sabon hotuna ita da yarta Fatima

Matar tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Sani Abacha tayi shar a sabon hotuna ita da yarta Fatima

Matar tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Sani Abacha tayi shar a sabon hotuna ita da yarta Fatima
NAIJ.com
Mailfire view pixel