Buhari ya kori mahafina saboda Kirista ne, musulmai kawai yake so – Haifaffen cikin Babachir Lawal

Buhari ya kori mahafina saboda Kirista ne, musulmai kawai yake so – Haifaffen cikin Babachir Lawal

-Yaron Babachir David Lawal da tuhumar Buhari da nuna bangarancin addini

-Yace ai an dakatad da mahaifinsa ne saboda mabiyi addinin Kirista ne

Wata magana da ake jinginawa yaron SGF Babachir David Lawall da aka daura a shafin sada ra’ayi da zumuntan Tuwita ya tayar da kura a kafofin yada labarai.

Yaron Babachir, wanda shugaba Buhari ya dakatar kwanakin nan yayi ikirarin cewa shugaba Muhammadu Buhari na son musuluntar da wannan gwamnati.

Buhari ya kori mahafina saboda Kirista ne, musulmai kawai yake so – Haifaffen cikin Babachir Lawal

Buhari da Babachir Lawal

Wannan magana ya sanya mutane da dama sukayi ca akan yaron mai suna, Suleiman inda yayi tufka da warwara bayan ya taba cewa Buhari zai lashe zaben 2019 kum zai sae dauko mahaifinsa a matsayin sakataren gwamnatin tarayya.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya halarci sallar Juma'a a yau

NAIJ.com tayi kokarin tattaunawa da yaron amma har yanzu bata samu dama ba.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Karanta yadda Yansanda suka rusa cibiyoyin matsafa da yan ƙungiyar Asiri a Legas

Karanta yadda Yansanda suka rusa cibiyoyin matsafa da yan ƙungiyar Asiri a Legas

Yansanda sun rugurguza matattaran matsafa guda 5 a jihar Legas (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel