Banyi nadamar zuwa na Amurka ba - Rahma Sadau

Banyi nadamar zuwa na Amurka ba - Rahma Sadau

- Jaruma Rahma Sadau ta musanta zargin da akeyi ma ta cewa tayi danasanin zuwa kasar America.

- Acewar jarumar ba wani da nasani da nayi domin adalilin sana'a naje bada niyar shashanci ba.

Amma abinda nasan nace shine, "tabbas akwai banbanci tsakanin America da Nigeria awajen yin fim," banbancin abayane yake. idan kai bahaushe ne to kayi sana'ar fim din hausa yafi maka amfani. domin shine wanda zai kare mutuncin mutum.

Dan haka a ra'ayina Hausa fim yafi min American fim, amma awajen hausawa. kuma ni da America gwara kasata Nigeria. wannan maganar nasan kawai na fada amma jama'a sai suka canja min magana.

Legit.ng ta sake samun labarin cewa tace sannan zanyi amfani da wannan damar nayi godiya zuwaga Ali Nuhu, Sani Danja da sauran mutanen da suke kokari awajen ganin nadawo masana'antar hausa fim.

Banyi nadamar zuwa na Amurka ba - Rahma Sadau
Banyi nadamar zuwa na Amurka ba - Rahma Sadau

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya sake daukar wasu alkawura

Wannan maganace daga bakin jaruma Rahma Sadau wanda tayi a dandalinta na sada zuminchi a Instagram.

A wani labarin kuma, Jaruma Rahma Sadau ta maka Nafisa Abdullahi a kotu. wanda tace tana neman hakin ta agun Nafisa Abdullahi. Wanda tace ta hana ta kudin ta har naira dubu tamanin da tara. Wanda Rahma Sadau taba Nafisa Abdullahi domin ta fito acikin fim din ta maisuna RARIYA. Amma har aka gama yin fim din Nafisa Abdullahi bata fito koda sau daya acikin fim din ba.

Anayin wannan sharia'a ne akotun Nomans land dake Kano State. Wakiliyar mu ta kotu Sadiya Rk Panshekara ta ruwaito mana cewa: za'aci gaba da sauraron shar'ar ranar Litinin.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Bayanan yan wasa akan masu tona asiri masu cin hanci da rashawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel