Matasa sun far ma Amosun, Akeredolu a taron jana’izar Isiaka Adeleke

Matasa sun far ma Amosun, Akeredolu a taron jana’izar Isiaka Adeleke

-Wasu matasa sun ci mutuncin gwamnaoni a taron jana’iza

-Sun kifar da rumfan da gwamnonin ke zaune ciki saboda wata Idiat Babalola

Wasu matasa masoya marigayi sanata Isiaka Adeleke sun rusa rumfa akan Amosun, Akeredolu, Oyinlola saboda a kori Idiat Babalola, wacce Gwamna Rauf Aregbesola zai nada kwamishana.

Idiat Babalola na zaune cikin manyan mutane wanda ya kunshi kanin marigayin, Deji Adeleke, inda wasu matasa suka fitittiketa wadanda sue zargin cewa wasu jigogin APC ne suka sanyawa marigayin guba ya mutu.

Matasan sunce, ana shirin nada Idiat a matsayin mataimakin gwamnan jihar a zaben da za’a gudanar na gaba.

YANZU-YANZU : Matasa sun far ma Amosun, Akeredolu a taron jana’izar Isiaka Adeleke

Isiaka Adeleke

Rikicn ya fara ne lokacin wasu suka hango Babalola inda suka bukaci a koreta daga taron jana’izar.

Duk da hakurin da iyalan marigayin suka bada , matasa sun lashi takobin cewa sai ta bar taron.

KU KARANTA: Soji sun kawar da harin Boko Haram a Adamawa

Matasa suka faru girgiza rumfan inda gwamna Amosun, Akeredolu, Olagunsoye Oyinlola da Deji Adeleke ke zaune.

Daga baya sai gwamna Amosun ya rakata waje tare da jami’an tsaronsho inda matasa ke jifanta da mangoro.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Labarin wani mutumin Arewa da yadda yake neman na abinci a Legas

Labarin wani mutumin Arewa da yadda yake neman na abinci a Legas

Labarin wani mutumin Arewa da yadda yake neman na abinci a Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel