Lionel Messi ya wulakanta Real Madrid har gida

Lionel Messi ya wulakanta Real Madrid har gida

– Barcelona ta doke Real Madrid a gidan ta

– Real Madrid ta sauko daga saman teburin La-liga

– Messi ya nuna kan sa a wasanna Elclasico

Dan wasan Barcelona watau Lionel Messi ya kara nunawa Duniya kan sa inda ya lallasa Kungiyar Real Madrid har gida a wasan da suka kara jiya. Lionel Messi ya ci wa Barcelona wasa ana daf da tashi.

Lionel Messi ya wulakanta Real Madrid har gida

Lionel Messi rusawa Real Madrid lissafi

Yanzu haka Messi na da kwallaye 500 a rayuwar sa, sai dai magoya bayan Real Madrid ba za su ci da dadin wannan ba ganin a gaban su aka yi. Real Madrid dai ta samu jan kati a wasan ta hannun Sergio Ramos.

KU KARANTA: An nemi a doke wani Gwamna a Janaiza

Lionel Messi ya wulakanta Real Madrid har gida

Messi ya doke Real Madrid a gida

Hakan na kuma nufin cewa Barcelona ta doke Real Madrid daga saman teburin gasar La-liga sai dai Real Madrid na da wasa guda da yayi kwantai. An dai dade Dan wasa Messi bai samu galaba a kan Real Madrid ba sai wannan karo.

A wancan makon NAIJ.com ta kawo maku cewa an yi waje da Kungiyar Barcelona daga Gasar UEFA Champions league na zakarun Nahiyar Turai na kakar bana inda su ka fafata da Juventus. Yanzu Juventus ta karasa zagaye na gaba za ta gamu da Monaco.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hanyar samun kudi a Najeriya

Source: Hausa.naij.com

Related news
Kungiyar Kwallon Kafa Ta Manchester United Ta Kuma Kafa Tarihi Bayan Samun Kazamar Riba Da Babu Kungiyar Data Taba Samu

NAIJ.com
Mailfire view pixel