Masu cutar HIV na neman agajin gaggawa a Najeriya

Masu cutar HIV na neman agajin gaggawa a Najeriya

- Sama da mutane miliyan 3 ke dauke da kwayoyin cutar HIV a Najeriya, kuma mutane 900,000 ne kawai ke samun damar shan magani na kashe kaifin cutar

- Hukumar NACA ta ce da dama masu dauke da cutar yanzu a Najeriya basa iya samun magani a dalili na karancin tallafi

- Kimani jihohi 10 ne cutar HIV ta fi kamari a kasar

Sama da mutane miliyan 3 ke dauke da kwayoyin cutar HIV wanda ke karya garkuwar jikin dan Adam a Najeriya kuma mutane 900,000 ne kawai ke samun damar shan magani na kashe kaifin cutar a Najeriya.

Hukumar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV/AIDS wato NACA a Najeriya ta nuna cewar da daman masu dauke da cutar yanzu basa iya samun magani a dalili na karancin tallafi da aka saba samu daga cibiyoyin duniya daban daban, sannan kuma gwamnatin Najeriya bata hobbasar da ta kamata kan yaki da cutar.

Gwamantin Najeriya dai na bada kashi 20 cikin dari ne kawai ta ke bayarwa adadin da ba ya isa. Wata mata mai dauke da kwayar cutar HIV a Najeriya ta ce babban kalubale da ke gabansu shi ne yadda za su samu maganin da ke kashe kaifin cutar ko kuwa su kasance cikin barazanar karewa.

Masu cutar HIV na neman agajin gaggawa a Najeriya
Magungunan cutar HIV

KU KARANTA KUMA: Babban hafsan sojin Najeriya ya kai ziyara kasar Brazil (Hotuna)

Legit.ng ta gano cewa jihar Ribas dai ta kasance cikin 10 na wadanda cutar ta fi kamari a kasar ta Najeriya, wannan ya sanya masu fafutikar tallafa wa masu cutar HIV ke kira ga gwamnati ta kai musu agaji cikin gaggawa, kasancewar a jihar ta Ribas ma kananan hukumomi 3 ne kawai ke tallafawa mutanen cikin 23 na jihar.

NACA dai ta ce za ta ci gaba da jan hankalin kungiyoyi da ke tallafawa a wannan yaki da cutar ta HIV mai halaka jama'a.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku duba alamomin da ya kamata a zani kana bukatar ka je gwaji HIV / AIDS

Asali: Legit.ng

Online view pixel