An gudu ba’a tsira ba: Babachir zai gurfana gaban majalisar dattawa

An gudu ba’a tsira ba: Babachir zai gurfana gaban majalisar dattawa

- Majalisar dattijai ta sake gayyatan Babachir David ya gurfana gabanta

- A satin daya gabata ne shugaba Buhari ya sallami Babachir David daga mukamin sakataren gwamnati

Majalisar dattawa ta bukaci korarren sakataren gwamnati Babachir David Lawal daya gurfana a gabanta don amsa tarin zarge zargen dake kansa kan badakalar naira miliyan 200 na kwangilar sare ciyawa daya baiwa kamfaninsa Rholavision.

Majalisar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa ta bakin shugaban kwamitin kula da yan gudun hijiran yankin Arewa maso gabas, Sanata Shehu Sani dake binciken badakalar.

KU KARANTA: Hukumar EFCC tayi caraf da likitan Goodluck, ta tasa ƙeyarsa zuwa kotu

Shehu Sani ya bayyana cewar suna bukatar Babachir ya bayyana gaban kwmaitin a ranar Alhamis da misalin karfe 10 na safe.

An gudu ba’a tsira ba: Babachir zai gurfana gaban majalisar dattawa

Babachir David

Sa’annan kwamitin ta aike ma Babachir da wasikar gayyata wanda ta samu sa hannun akawun kwamitin Lawal Bungudu, kamar yadda NAIJ.com ta gano.

Dama dai tun a bayan kwamitin bayan kammala wani bincike da tace tayi akan zargin, ta kama Babachir da laifin almundahana, inda har ma ta shawarci shugaban kasa daya sallame shi daga aiki.

An gudu ba’a tsira ba: Babachir zai gurfana gaban majalisar dattawa

Wasikar gayyatar Babachir

Amma kuma ko a baya ma Babachir din bai amsa kiran majalisar ba na ya gurfana gabanta, inda ya musanta samun takardar gayyatar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram

Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram

Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram
NAIJ.com
Mailfire view pixel