366

USD/NGN

Gwamnoni 5 da su ka hana a tsige Sarki Muhammadu Sanusi II

Gwamnoni 5 da su ka hana a tsige Sarki Muhammadu Sanusi II

– Kwanaki aka fara binciken Masarautar Kasar Kano

– Wannan na cikin wani barazana na dakatar da Sarkin

– Tun ba yau ba akwai kishin-kishin cire Sarki Sanusi II

Kwanakin baya NAIJ.com ta fara samun jita-jitar cewa wasu Gwamnonin Arewa na kokarin tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Har aka ce wasu daga cikin Gwamnonin sun yi wani taro game da Sarkin a kasar China.

Daga baya aka koma ana zargin Masarautar da barnatar da makudan kudi inda aka nemi tayi bayani .

Gwamnoni 5 da su ka hana a tsige Sarki Muhammadu Sanusi II

Gwamnoni sun hana a tsige Sarki Sanusi II

Yanzu haka muna samun labari daga Daily Trust cewa wasu Gwamnonin Arewa 5 su ka shiga tsakanin rikicin Sarkin Kano Sanusi II da kuma Gwamnan Jihar Dr. Abdullahi Ganduje a wani zama da aka yi a Kaduna.

KU KARANTA: Sarki Sanusi bai yi daidai ba Inji Babban Malami

Gwamnoni 5 da su ka hana a tsige Sarki Muhammadu Sanusi II

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Gwamnonin su ne dai Malam Nasir El-Rufai, Aminu Waziri Tambuwal, Kashim Shettima, Abubakar Sani Bello da kuma Aminu Bello Masari. Gwamnonin sun yi wannan zama ne a Gwamnan Jihar Kaduna tare da Gwamna Ganduje da wani Sarki da kuma Masarautar Kano.

Sai da aka dauki dogon lokaci dai kafin a shawo kan Gwamnan da yayi hakuri da abin da ya faru tsakanin sa da Sarkin inda ya rika sukar sa a fili duk da cewa Gwamnatin Jihar Kano ce ta nada sa. Hakan dai zai kawo zaman lafiya a Yankin Arewacin kasar gudun abin kunya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Jama'a na nuna goyon bayan Buhari

Related news
Dan shekara 10 ya labarta yadda ya zama gawurtaccen dan fashi da makami

Dan shekara 10 ya labarta yadda ya zama gawurtaccen dan fashi da makami

Dan shekara 10 ya labarta yadda ya zama gawurtaccen dan fashi da makami
NAIJ.com
Mailfire view pixel