365

USD/NGN

Manchester United ta tuna da ‘Yan Najeriya da su ka rasu

Manchester United ta tuna da ‘Yan Najeriya da su ka rasu

– Kungiyar Manchester United ta Ingila ta tuna da ‘Yan Najeriya da su ka rasu

– ‘Yan kasar sun rasu ne kwanaki wajen kallon wasan Kungiyar

– Man Utd din da tayi makokin wadannan gwaraza na wani dan lokaci

Kungiyar wasan kwallon kafa ta Manchester United da ke Kasar Ingila tayi makokin ‘Yan Najeriya.

Manchester United tuna da ‘Yan Najeriya da su ka bar Duniya wajen kallon wasan su.

Wannan abu dai ya faru ne a Garin Kalaba.

Manchester United ta tuna da ‘Yan Najeriya da su ka rasu

Kungiyar Man United ta tuna da ‘Yan Najeriya

A wasan wannan makon ne Kungiyar Manchester United ta Kasar Ingila tayi makokin wasu ‘Yan Najeriya da su ka rasu wajen kallon kwallon wasan Kungiyar na Gasar UEFA Cup tare da Kungiyar Anderlecht.

KU KARANTA: An kama wadanda su ka nemi su kashe Sanata

Manchester United ta tuna da ‘Yan Najeriya da su ka rasu

'Yan wasan Kungiyar Manchester United

Kungiyar tayi ta’aziya a shafin ta na Twitter tun sa’ilin da abin ya faru a Ranar Juma’a washegari. Haka kuma Shugaba Buhari da Jakadan kasar a Najeriya ya mika gaisuwar sa inda yake jajantawa Iyalan mutanen. Wasu dai sun mutu har lahira bayan igiyar wuta ta fado masu ana tsakar wasa.

A wani wasan damben Duniya da aka yi a Kasar Ingilar wani ainihin Dan Najeriya ne yayi nasara. Anthony Joshua ya gabje Wladmir Klitschko a damben Duniyar da aka gwabza a filin wasan Wembley.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

'Yan yankan kai su yi gaba da yaron wannan mata

Related news
Dalilai 4 da su ka sa Malaman FCE ke shirin bin sawun ASUU zuwa yajin aiki

Dalilai 4 da su ka sa Malaman FCE ke shirin bin sawun ASUU zuwa yajin aiki

Yajin aiki: Dalilai 4 da su ka sa Malaman FCE ke shirin bin sawun ASUU
NAIJ.com
Mailfire view pixel