Majalisa ta yi amai ta lashe kan tantance kwamishinonin zabe

Majalisa ta yi amai ta lashe kan tantance kwamishinonin zabe

-Majalisar Dattawa ta fara tantance kwamishinonin hukumar zabe mai zaman kanta

- Sanata Ahmad Lawan ya gabatar da bukatar sake duba batun tantance kwamishinonin

- Bukola saraki ya umarni sanata Suleman Nazifi kan ya shugabanci kwamitin hukumar zabe na majalisar

Majalisar Dattawa ta yi amai ta lashe inda ta fara tantance kwamishinonin hukumar zabe mai zaman kanta, INEC bayan da 'yan majalisar suka jingine sunayen don nuna rashin Jin dadinsu kan yadda shugaba Buhari ya ki mutunta bukatarsu na cire Ibrahim Mgu daga hukumar EFCC.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, shugaban zauren majalisar, sanata Ahmad Lawan ne ya gabatar da bukatar sake duba batun tantance kwamishinonin.

KU KARANTA KUMA: LABARI DA DUMI-DUMI: Shugaba Buhari ya koma bakin aikinsa

Shugaban marasa rinjaye na majalisar, sanata Godswill Akpabio nan take ya maramasa baya wanda kuma shugaban majalisar, Bukola saraki nan take ya umarni sanata Suleman Nazifi daga jihar Bauchi kan ya shugabanci kwamitin hukumar zabe na majalisar don duba batun kasancewa, an dakatar da ainihin shugaban kwamitin, sanata Ali Ndume.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon rikicin takardar shaidar sanata Dino Melaye.

Source: Hausa.naij.com

Related news
Allah Sarki: Wata dattijuwa ta samu waraka daga makanci sanadiyar aikin agajin lafiya na soji

Allah Sarki: Wata dattijuwa ta samu waraka daga makanci sanadiyar aikin agajin lafiya na soji

Dattijuwa ta samu warakar makanta bayan aikin agajin Soji na inganta lafiya a Ribas
NAIJ.com
Mailfire view pixel