Abin tausayi: Ana neman taimakon ‘yan Najeriya da gaggawa (Hotuna)

Abin tausayi: Ana neman taimakon ‘yan Najeriya da gaggawa (Hotuna)

- Malam Fatihu Abubakar ya rasa mazakutarsa ga gobarar wuta a garin Tsafe

- Ana bukatar taimakon gaggawa daga al’umma don a taimaka masa yin jinyar konewar

- Likitoci sun ce akalla aikin zai ci kimanin naira 150,000

Malam Fatihu Abubakar Magazu dake zaune a garin Tsafe jihar Zamfara a unguwar Magazu bakin titi, ya na bukatar taimakon gaggawa daga al’umma sakamakon wata konewa da ya yi.

Wannan bawan Allah tun daga cikinsa har zuwa cinyoyinsa sun kone, hatta mazakutarsa ta kone.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari wannan Abu ya faru ne sanadiyar wani iftila'in gobara da Allah ya sauko masa da ita. An je asibitin garin Tsafe amma ba su karbe shi ba, sun ce ba su da kayan aikin da za a yi masa wannan aikin.

Abin tausayi: Ana neman taimakon ‘yan Najeriya da gaggawa (Hotuna)

Malam Fatihu Abubakar Magazu da yan uwarsa yayin da ake masa maganin gargajiya a gida

Haka ya sa aka koma da shi gida ana yi masa na gargajiya, sakamakon rashin karfi da rashin kudin da za su je asibitin da za a iya masa aiki.

KU KARANTA KUMA: Wuta a hukumar leken asiri ta kasa (Karanta)

Likitoci sun ce akalla aikin zai ci kimanin naira 150,000. Wajen da ya kone ya fara rubewa.

Malam Fatihu na neman taimakon gaggawa ga al'umma akan a taimaka masa.

Ga mai son taimaka masa za ku iya amfani da wannan Account Lamba:

ACC NO: 0178581234

NAME: Haruna Said

BANK: GTBank

Ko Kuma wannan Lambar waya dan karin bayani Mashkur Alkali Tsafe,

07034638905.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon rikicin kudancin Kaduna shafi na farko

Source: Hausa.naij.com

Related news
Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Senata Misau a kotu bisa zarginsa da yada karerayi kan Sifeta Janar Idris

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Senata Misau a kotu bisa zarginsa da yada karerayi kan Sifeta Janar Idris

Labari da duminsa: Sanata Misau ya gurfana gaban kotu bisa zargin da ya jefa kan Sifeta Janar na 'yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel