An gano gawar jariri kunshe cikin buhu a bola wannan jihar (Karanta)

An gano gawar jariri kunshe cikin buhu a bola wannan jihar (Karanta)

An gano gawar wani jariri cikin buhun shara a wata matartarar shara dake kusa da kasuwar Alagbado dake a can jihar Lagos.

Wurin tattara sharar na kusa da gidan Talabijin na AIT, dake kan titin da ake kira Market Road.

Wakilin kamfanin dillancin labarai na ƙasa wanda ya ganewa idonsa abin da yafaru yace, gawar yaran ta gangaro daga cikin buhun lokacin da ake saka buhun cikin motar ɗaukar shara.

NAIJ.com ta samu labarin Masu ɗebe sharane suka ga yaron inda suka sanar da mutanen kasuwar abinda ke faruwa.

An gano gawar jariri kunshe cikin buhu a bola wannan jihar (Karanta)

An gano gawar jariri kunshe cikin buhu a bola wannan jihar (Karanta)

Mutanen kasuwar maza da mata sun taru, inda suka riƙa tsinuwa ga waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki.

Wani Jami’in ɗan sanda dake wurin ya faɗawa kamfanin dillancin Labarai na Najeriya NAN, cewa za a gudanar da bincike domin gano waɗanda keda hannu a aikata wannan abin baƙin ciki.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Wani Babban malami a jihar Kano ya kalubalanci masu sukar Kasar Sudiya akan kafa cibiyar tace Hadisai

NAIJ.com
Mailfire view pixel