366

USD/NGN

Sojoji sun tabbatarda kashe jagororin Boko Haram a kusa da Sambisa

Sojoji sun tabbatarda kashe jagororin Boko Haram a kusa da Sambisa

- Sojoji sun kashe shuwagabannin kungiyar Boko Haram a dajin Sambisa

- An kona ragowar makaman da yan ta'addan suka bari a gudun tsira da suke yi

Manyan hukumomin sojoji daga Abuja sun bada jawabi ranar Alhamis cewa an kashe dayawa daga kwamandojin boko haram a hare-haren da suka kai hakan ya aukune a nakaltowan NAIJ.com a harin da operation Deep Punch suka kai a wata mafakar yan ta'addan a yankin sambisa.

A fadin darakta,kuma mai yada labaran sojojin, Brigadiya Janar Sani Usman, harin da tawagar sojojin sama suka kai na Zama Lafiya Dole ya rusa manya-manyan mafakar yan ta'ardan ne tareda bata wasu daga makaman su a mafi yawancin yankin Sambisa na Balla da Parisu.

KU KARANTA: YANZU-YANZU: Rundunar Sojin Najeriya ta raunata Shekau, ta kuma kashe mataimakin sa

Brigadiya Janar Usman yace: “Rahotanni sun gabata game da raunata jagororin Boko Haram kamar yarda kuka sani yan Boko Haram a kan tsere suke ,amma yanzu kam babu mafaka a garesu.

“Muna tabbatarmuku da cewa tsare-tsare na nan na tafiya a kokarin kawarda tarzomar arewa maso gabashin Najeriya.

“Sojojin saman Najeriya na kokari gurin dacewa da hare-haren da suke kaiwa da rusa mafakokin yan Boko haram,hakan kuma wato abin yabo ne da karfafa domin cigaba da wanzuwar lafiya dayake haifarwa a yankin.

''Bincike na cigaba da gudanuwa gameda yawan wadan da aka raunata daga tawagar yan ta'adda din a kokarin tabbatarda alaka tsakanin sojojin da farar hula, makarantar sojoji ta musamman -Nigerian Army Special Forces School (NASFS) sun toni ruwan sha ranar Laraba a Buni Yadi, jihar Yobe wanda Brigadiya Janaral MG Ali, kwamandan NASFS ya sanya a karkashin kulawar Lawal Abubakar Adam na Fulatari a Buni Yadi.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Related news
Hotunan barnar da ruwan sama yayi jihar Yobe

Hotunan barnar da ruwan sama yayi jihar Yobe

Hotunan barnar da ruwan sama yayi jihar Yobe
NAIJ.com
Mailfire view pixel