Manyan hafsoshin sojin Najeriya sun ziyarci a fadar shugaban kasa

Manyan hafsoshin sojin Najeriya sun ziyarci a fadar shugaban kasa

-A yau Juma'a 5 ga watan Mayu ne aka hangi shuwagabannin sojin kasar nan a fadar shugaban kasa

-Manyan hafsoshin basu bayyana dalilin halartan su fadar shugaban kasar ba

Wani rahoto na jaridar Vanguard ya tabbatar da hangen keyar jiga jigan hafsoshin tsaron kasar nan a fadar shugaban kasa a yau Juma’a 5 ga watan Mayu.

Hafsohin sun hada da babban hafsan soji Janar Olanisakin, shugaban hafsan sojin kasa, Janar Tukur Buratai, shugaban hafsan sojin ruwa Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Iba da babban hafsan sojin sama Air Vice Marshal Sadique Abubakar.

KU KARANTA: Za’a ci tarar duk wanda ya ci mutuncin tutar Najeriya maƙudan kuɗi, Karanta

Sai dai majiyar NAIJ.com tace har zuwa lokacin hada rahoto ba’a san takamaimen dalilin zuwansu fadar shugaban kasar ba, sa’annan basu yi ma manema labaru wani bayani ba dangane da ziyarar tasu.

Manyan hafsoshin sojin Najeriya sun ziyarci a fadar shugaban kasa

Manyan hafsoshin sojin Najeriya

Bugu da kari ba’a tabbatar da ko sun samu damar ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba don bada rahoton ayyukan da suke gudanarwa, abinda aka sani kawa shine an hange su suna fita daga fadar shugaban kasa da misalin karfe 9 na safiyar juma’a.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rikcin kudancin Kaduna

Source: Hausa.naij.com

Related news
Labari da duminsa: Sanata Misau ya gurfana gaban kotu bisa zargin da ya jefa kan Sifeta Janar na 'yan sanda

NAIJ.com
Mailfire view pixel