366

USD/NGN

Yanzu-Yanzu: ‘Yan matan Chibok 82 sun dira a filin jirgin sama a Abuja (Hotuna)

Yanzu-Yanzu: ‘Yan matan Chibok 82 sun dira a filin jirgin sama a Abuja (Hotuna)

- 'Yan matan Chibok 82 sun sauka yanzu a filin jirgin sama da ke birnin tarayya Abuja

- Alhaji Abba Kyari ya karbi ‘yan matan a madadin shugaban kasar a filin jirgin sama ta Abuja

- Shugaba Muhammadu Buhari zai karbi bakonci 'yan matan da aka sako a fadar gwamnati

'Yan matan Chibok 82 sun sauka yanzu a filin jirgin sama da ke birnin tarayya Abuja. Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin tarayya, Alhaji Abba Kyari ya karbe su a madadin shugaban kasar a filin jirgin sama ta Abuja.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, mataimakin na musammam kan harkokin yada labarai ga shugaban Najeriya, Mallam Garba Shehu ya ce a ranar Lahadi, 7 ga watan Mayu, cewa shugaba Muhammadu Buhari zai karbi 'yan matan da aka sako a fadar gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Ra’ayin Jama’a game da ceto ‘Yan matan Chibok

A ranar Asabar, 6 ga watan Mayu ne gwamnatin Najeriya ta sanar cewa ta yi musayar mayakan Boko Haram da kungiyarsu don kubutar da 'yan matan sakandaren Chibok 82.

Yanzu-Yanzu: ‘Yan matan Chibok 82 sun dira a filin jirgin sama a Abuja (Hotuna)

‘Yan matan Chibok 82 a lokacin da zasu shiga jirgi zuwa abuja

Barkan mu ‘yan Najeriya da wannan nasara.

Yanzu-Yanzu: ‘Yan matan Chibok 82 sun dira a filin jirgin sama a Abuja (Hotuna)

‘Yan matan Chibok 82 sun dira a filin jirgin sama a Abuja

Yanzu-Yanzu: ‘Yan matan Chibok 82 sun dira a filin jirgin sama a Abuja (Hotuna)

Shugaba Buhari da mataimakinsa Osinbajo da wasu 'yan matan Chibok

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon zanga-zanga a Legas kan 'yan matan Chibok da Boko Haram suka sace

Related news
Hotunan barnar da ruwan sama yayi jihar Yobe

Hotunan barnar da ruwan sama yayi jihar Yobe

Hotunan barnar da ruwan sama yayi jihar Yobe
NAIJ.com
Mailfire view pixel