Toh fa: Rikici ta sake barkewa a jihar Taraba

Toh fa: Rikici ta sake barkewa a jihar Taraba

- Wata sabuwar rikici ta barke tsakanin Fulani makiyaya da kuma wasu kabilun Kuteb a jihar Taraba

- An samu hasarar rayuka da dama wasu kuma da dama sun samu raunuka kuma an kona dabbobin

- Har yanzu makiyaya fiye da 150 ne ba’a san inda suke ba

Wani rikici ya barke tsakanin Fulani makiyaya da kuma wasu kabilun Kuteb a karamar hukumar Ussa da kuma wani bangare na karamar hukumar Takum dake kudancin jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya.

Rahotanni daga jihar na cewa an samu hasarar rayuka da dama wasu kuma da dama sun samu raunuka kuma an kona dabbobin biyo bayan rikicin daya afku, tuni aka tura karin jami’an tsaro zuwa yankunan da abun ya faru,domin tabbatar da doka da oda.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Miyetti Allah tayi tir da dokar hana kiwo na gwamnatin Jihar Binuwai

Kamar yadda Legit.ng ke da labara, kawo yanzu akwai wasu makiyaya fiye da 150, da ba’a san inda suke ba, kamar yadda shugaban kungiyar Miyetti Allah ta kasa reshen jihar Taraba Jauro Sahabi Mahmud Tukur ya bayyanawa manema labarai a Jalingo fadar gwamnatin jihar Taraba, inda ya bukaci hukumomin tsaro dasu kai musu dauki.

Toh fa: Rikici ta sake barkewa a jihar Taraba
Wasu gidace da dabbobi da aka kona a lokacin rikicin

Haka zalika wani da ya ziyarci yankunan Bello Ahmadu Bela daga kungiyar Tabital Puulaku kira ya yi ga gwamnatin jihar Taraba da ta hanzarta daukan matakin gaggawa ganin yadda lamarin ke neman kazancewa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon rikicin kudancin Kaduna kashi na biyu

Asali: Legit.ng

Online view pixel