Za'a sake sako wasu karin yan matan Chibok nan ba da dadewa ba - Minista

Za'a sake sako wasu karin yan matan Chibok nan ba da dadewa ba - Minista

- Ministan sadarwa Adebayo Shitu ya bayyana haka yayin taron shekara-shekara karo na uku, na kungiyar al’ummar musulmai dake kudu maso yammacin Najeriya.

- Yayin da yayi kira ga yan Najeriya, kan suyi addu’ar samun sauki ga Shugaban Kasa Muhammad Buhari, ministan yace gwamnati na aiki tukuru wajen dora kasarnan kan hanyar cigaba.

Ministan sadarwa Adebayo Shitu ya bayyana haka yayin taron shekara-shekara karo na uku, na kungiyar al’ummar musulmai dake kudu maso yammacin Najeriya.

Yayin da yayi kira ga yan Najeriya, kan suyi addu’ar samun sauki ga Shugaban Kasa Muhammad Buhari, ministan yace gwamnati na aiki tukuru wajen dora kasarnan kan hanyar cigaba.

Ya kuma kara da cewa a karon farko cikin tarihin kasarnan fannin sadarwa ya samar da kaso 10 na jimillar tattalin arzikin kasa.

Za'a sake sako wasu karin yan matan Chibok nan ba da dadewa ba - Minista

Za'a sake sako wasu karin yan matan Chibok nan ba da dadewa ba - Minista

KU KARANTA: Darajar Naira ta kara ruguzowa a kasuwanni

Shitu yace wutar lantarki ta inganta, an samu dai daito a farashin man fetur,raguwar cin hanci da rashawa, da kuma warware rikicin Neja Dalta.

NAIJ.com ta samu labarin cewa a nasa jawabin Shugaban kungiyar Sakariyau Babalola,ya shawarci gwamnati da kada tayi kasa a gwiwa a shirin da take na tallafawa talakawa da kuma marasa aikin yi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Senata Misau a kotu bisa zarginsa da yada karerayi kan Sifeta Janar Idris

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Senata Misau a kotu bisa zarginsa da yada karerayi kan Sifeta Janar Idris

Labari da duminsa: Sanata Misau ya gurfana gaban kotu bisa zargin da ya jefa kan Sifeta Janar na 'yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel