Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara yayi magana kan mulkin gargajiya

Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara yayi magana kan mulkin gargajiya

Kakakin majalisar wakilai ta Najeriya, Yakubu Dogara, ya nanata kira na da a dawo wa da masu mulkin gargajiya qarfin fada aji ga talakawansu a hukumance

Su dai Sarakunan gargajiyar sun rasa qarfin fada aji a hukumance tun zuwan dimokuradiyya

Talakawansu har yanzu sun fi ganin kima da mutuncin su fiye da 'yan siyasa, sannan kuma sun fi kusa da talakka.

Kakakin Majalisar, yayi wannan Kira ne a Birnin Kebbi a lokacin da ake bikin nadin daya daga cikin mambobinsu a Majalisa, Alhassan Ado Doguwa, bulaliyar Majalisa.

Mataimakin Shugaban, Umar Jibril ne ya wakilce shi a Ranar lahadin nan, a wurin nadin sarautar a fadar Sarkin Kebbi, Wanda Gwamna Atiku Bagudu yake halarta.

Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara yayi magana kan mulkin gargajiya

Yakubu Dogara

Ya Kara da cewa, wannan Doka da za'a Samar, Zata Kara wa masu sarautar qarfin fada aji, kuma Zata fi kusantar da talakka ga masarauntansu.

Ya kuma yi Kira da a Samar da Kayan Noma da wuri kafin damina ta sauka domin habaka tattalin arzikin yankin, da samar da abinci ga jama'a.

Source: Hausa.naij.com

Related news
Labari da duminsa: Sanata Misau ya gurfana gaban kotu bisa zargin da ya jefa kan Sifeta Janar na 'yan sanda

NAIJ.com
Mailfire view pixel