An ajje tsohon ministan gwamnatin Jonathan na Abuja a gidan kaso

An ajje tsohon ministan gwamnatin Jonathan na Abuja a gidan kaso

- Bala Muhammad shine ministan Abuja a lokacin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan

- An ajje ministan a kurkuku na Kuje, da ke Abuja

- Ana kuma tuhumarsa da laifin kin bayyana dukkan dukiyarsa, kamar yadda dokar aiki tace

A dazu dazun nan ne wata babbar kotu a Abuja, ta ce a garkame tsohon ministan Abuja a kurkuku da ke Kuje a Abujar, sakamakon tuhumce tuhumce na cin hanci da rashawa da yake fuskanta, tun bayam saukar su daga gadon mulki shekaru biyu da suka gabata.

Kotun na kuma bukatar a kawo mata kwararan hujjoji na qarin tuhuma game da kin bayyana ainahin yawan dukiyarsa, wadda hakan ka iya aika shi zuwa kotun duba laifukan ma'aikata ta code of conduct tribunal, domin bin kadi.

A kwanakin nan dai, mutanen tsohon Shugaba Goodluck na fuskantar tuhumce-tuhumce a kan irin wadannan laifuka na sata da wawura, wasu har ma a ga kudin a gidajensu.

Daga cikin wadanda aka rufe a kurkuku, akwai tsofaffin gwamnonin Neja da Jigawa, Aliyu Babangida da Sule Lamido, wanda wasu ke gani, bita da kulli ne kawai na siyasa, don basa cikin jam'iyya mai mulki, kuma domin lokutan zabe na qaratowa.

Source: Hausa.naij.com

Related news
Allah Sarki: Wata dattijuwa ta samu waraka daga makanci sanadiyar aikin agajin lafiya na soji

Allah Sarki: Wata dattijuwa ta samu waraka daga makanci sanadiyar aikin agajin lafiya na soji

Dattijuwa ta samu warakar makanta bayan aikin agajin Soji na inganta lafiya a Ribas
NAIJ.com
Mailfire view pixel