Karfin hali, ɓarawo da yin sata a caji ofis

Karfin hali, ɓarawo da yin sata a caji ofis

- A nan kuma wani sarkin karfin hali ne da yayi sata a ofishin yansanda a jihar Legas

- Sai dai ya shiga hannu, kuma yansandan sun gurfanar da shi gaban kuliya manta sabo

NAIJ.com ta samo rahoton wani matashi da aka gurfanar da shi gaban kotu sakamakon sata da yayi a ofishin yansanda dake Olosan, unguwar Mushin jihar Legas a lokacin da yake daure a ofishin.

Yansandan sun bayyana ma kotu cewar akwai wasu yan fashi da suka kama, suka garkame su a caji ofis.

KU KARANTA: Farar hula da ɗansanda sun baiwa hammata iska a Abuja

Amma cikin dare sai yan fashin suka kusta kai cikin sashin yaki da yan fashi na caji ofis din suka kwashe kudade da wayoyi guda biyu mallakan dansanda Femi Elebute da Shittu Babatunde, daga bisani kuma suka tsere.

Karfin hali, ɓarawo da yin sata a caji ofis

Caji ofis

Sai dai yansandan sun samu nasarar kama daya daga cikin yan fashin mai suna Onyeka Mba mai shekaru 22, kuma sun gurfanar da shi gaban kotu, sai dai Mba ya musanta tuhume tuhumen yansandan, daga nan ne alkali mai shari’a E.O Ogunkanmi ya bada belinsa akan N100,000.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli ta'asan da yansanda suka yi ma wata mata

Source: Hausa.naij.com

Related news
Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Senata Misau a kotu bisa zarginsa da yada karerayi kan Sifeta Janar Idris

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Senata Misau a kotu bisa zarginsa da yada karerayi kan Sifeta Janar Idris

Labari da duminsa: Sanata Misau ya gurfana gaban kotu bisa zargin da ya jefa kan Sifeta Janar na 'yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel