Da ɗumi ɗumi: Kotu ta bada belin tsohon minista, Bala Mohammed

Da ɗumi ɗumi: Kotu ta bada belin tsohon minista, Bala Mohammed

- Babban kotun birnin tarayya Abuja ta bada belin tsohon minista Bala Mohammed

- Kotun ta bada belin sa ne akan tsauraran sharudda da take bukatar ya cika

Babban kotu dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta bada belin tsohon ministan babban birnin tarayya Alhaji Bala Mohammed kauran Bauchi.

Alkalin kotun, mai sharia’a Abubakar Talba ya bada belin tsohon ministan ne akan zambar kudi naira miliyan 500 tare da mutane biyu masu mutunci da zasu tsaya masa, suma zasu biya naira miliyan 500 kowanne.

KU KARANTA: Kotu ta umarci a ɗaure mata tsohon minista Bala Muhammed a gidan yari

Mai shari’a Talba ya yanke cewar lallai sai daya daga cikin mutanen da zasu tsaya ma Bala Mohammed ya kasance dan majalisar dattijai, wato Sanata, dayan kuma kada ya gaza mai mukamin darakta a hukumar ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Da ɗumi ɗumi: Kotu ta bada belin tsohon minista, Bala Mohammed

Tsohon minista, Bala Mohammed

Bugu da kari Alkalin yace dole ne sai dukkanin mutanen da zasu tsaya ma tsohon ministan sun mallaki kadarori a babban birnin tarayya Abuja, tare da nuna shaidar biyan haraji na tsawon shekaru uku da suka gabata.

Daga karshe Alkalin ya umarci tsohon ministan daya ajiye fasfon sa na fita kasashen waje a hannun akawun kotu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga sabuwar hanyar tona barayi, kuma ka samu kudi

Source: Hausa.naij.com

Related news
Allah Sarki: Wata dattijuwa ta samu waraka daga makanci sanadiyar aikin agajin lafiya na soji

Allah Sarki: Wata dattijuwa ta samu waraka daga makanci sanadiyar aikin agajin lafiya na soji

Dattijuwa ta samu warakar makanta bayan aikin agajin Soji na inganta lafiya a Ribas
NAIJ.com
Mailfire view pixel