Hakar Bakin Man Najeria ya karu da ganga 274,000 a yini a watan Afrilu –OPEC

Hakar Bakin Man Najeria ya karu da ganga 274,000 a yini a watan Afrilu –OPEC

- Karuwar hakar bakin man Najeriya na nuni ga karuwar jari wa kungiyar tarayyar kasashen duniya masu hakar mai OPEC

- Bakin man da kasar Najeriya ke haka ya karu da ganga 274,000 a yini a watan Afrilu a cewar, Organisation of Petroleum Exporting Countries (OPEC) ranar Alhamis

Rahotanni sun nuna karuwar hakar bakin man a cewar OPEC kamar yarda NAIJ.com ta ruwaito na nuni ga karuwar jari wa kungiyar ta duniya baki daya.

A bayanan na OPEC a rahotanninsu na wata wata Ranar Alhamis da ta gabata sunce Najeriya an sanya samarda manta a kimanin ganga 1.484 miliyan a watan Afrilu daga ganga 1.21 miliyan a yini a watan mayu, wadannan bayanan sun samo asali ne daga tantancewa da tattaunawa da ita kasar ta Najeriya

A yayinda hakan ke kasancewa da Najeriya a gefe guda kuma kasar Angola na fuskantar Raguwar yawa na hakar man da takeyi zuwa ga Ganga 1.651 miliyan a yini a watan Afrilu,daga ganga 1.652 miliyan a yini a watan da ya gabata.

KU KARANTA: Da ɗumi ɗumi: Kotu ta bada belin tsohon minista, Bala Mohammed

Rahoton ya sake nuna cewa kasar Saudiyya wacca tafi kowa samar da man a tarayyar kasashe masu samar da mai ta samu kari itama a watan Afrilu gun samar da ganga 9.946 miliyan a yini daga 9.9 miliyan a yini a watan Maris.

Kasar Kuwait, kuma ta samu karin samar da yawan man ne daga ganga 10,000 a yini zuwa ganga 2.710 miliyan a yini.

Dubai nata ya karu daga ganga 15,000 a yini zuwa ganga 2.988 miliyan a yinin a watan Afrilu.

Samar da man na kungiyar OPEC na gaba daya ya ragu ne da ganga 18,000 a watan da ya gabata a rahoton NAIJ.com.

Kasashen da Raguwar hakar man ya shafa a kungiyar tarayyar mahakan man sun kunshi; UAE, Libya, Iraq and Iran, kari kuma ya auku a Najeriya da Sudiyya.

Shirye-shiryen samar da hanyoyin karuwar hakar man da magance raugwarsa na nan na gudanuwa a kungiyar ta OPEC domin cinma bukatun duniya baki daya.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Kalli bidiyon nuna goyon baya ga cigaban shugabancin buhari a 2019

Source: Hausa.naij.com

Related news
PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2

PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2

PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2
NAIJ.com
Mailfire view pixel