Neman izinin aure: Yarinya ta kai Ubanta kotu, ta nemi a hukunta shi

Neman izinin aure: Yarinya ta kai Ubanta kotu, ta nemi a hukunta shi

- Wata yarinya Khadija ta gurfanar da mahaifinta Ibrahim gaban kuliya manta sabo kan batun aure

- Yarinyar ta zargi mahaifin nata da kin amincewa tayi auri wanda take so

Wata budurwa mai shekaru 23, Khadija Ibrahim ta gurfanar da Ubanta Ibrahim Bassa gaban karamin kotu dake garin Karu, babban birnin tarayya Abuja don ya hanata auren wanda take so.

Jaridar Premium Times ta ruwaito yarinyar ta fada ma kotu cewa ita fa tana da mijin da zai aureta, amma mahaifinta yaki yarda ya amince da shi:

KU KARANTA: Majalisa ta kasafta naira biliyan 13 kuɗaɗen cin abinci da tafiye tafiye

“Yaki ya amince nayi aure, kuma ya kasa bani gamsashshen bayani, mutumin da nake son aura yayi kokarinsa na ganin ya hadu da mahaifina, amma yaki ya basu damar ganawa da shi.

“Dalilinsa kawai shine baya son na auri mutumin da ba Fulani ba, amma gaskiya ni ban gamsu ba, saboda ina son mutumin.” Inji yarinyar.

Daga nan sai yarinyar ta umarci kotu data tirsasa mahaifin ya bata daman auran wanda take so, mai suna Abdulhamidu.

Dayake amsa tuhumar dake kansa, Mahaifin yarinyar, Ibrahim Bassa yace “Gaskiya ne ban hadu da saurayinta ba, bana bari hadu saboda bana son shi, na gargadi yarinyata cewar aure fa ba abin wasa bane.

“Saboda mu a Fulani, idan zaka auri yar mu, sai mun san ka mun san danginka, kuma ni ina ganin tayi karama ta daukan ma kanta hukunci.” Kamar yadda majiyar Legit.ng ta kalato.

Bayan sauraren dukkan bangarorin, sai Alkali mai shari’a Abdullahi Baba ya dage sauraron karar zuwa ranar 29 ga watan Mayu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin ya kamata miji ya dinga satar duba wayan matarsa?

Asali: Legit.ng

Online view pixel