Sabon harin Fulani makiyaya ya kawo asarar rayuka a jihar Neja

Sabon harin Fulani makiyaya ya kawo asarar rayuka a jihar Neja

- Hare-Haren Fulani makiyaya ya zama ruwan dare a Najeriya

- Mahukunta sun kasa shawo kan lamarin

- Wasu lokutan ana zargin manoma da sauran kabilu da ta'azzara rashin jituwar al'ummun

Rahotanni daga jihar Neja ta arewacin Najeriya, na cewa, an sami sabuwar hatsaniya tsakanin jama'ar fulani makiyaya da kuma manoma a jihar Neja a garin Boso, wanda har ya jawo asarar rayuka.

Majiyar Legit.ng ta bada adadin a cewa mutane shida ne suka rasu a fadan, amma hukumar 'yan sanda a yankin ta ajje alkaluman a guda hudu kacal.

Sabon Harin Fulani Makiyaya ya kawo asarar rayuka a jihar Neja.
Sabon Harin Fulani Makiyaya ya kawo asarar rayuka a jihar Neja.

Hatsaniyar ta faru a lahadin nan, tsakanin 'yan kabilar Tugan a Paiko da kuma ta Fulani. Wannan shine hari na baya-baya bayan wanda ya faru a Mokwa a ranar asabar dinnan, wanda shi kuma mutane 21 ne suka rasa rayukaqnsu, a garin Epogi.

Anji dai cewa, fadan ya faro ne daga musu tsakanin samarin kabilun biyu, inda ya kai ga saurayi bafillace daba wa abokin hamayyarsa wuka, inda shi kuma mutanen sa suka kaishi asibiti, suka kuma dawo suka far ma jama'ar fulani na yankin.

Wannan abu sai ya tunzura sauran jama'ar kabilun, inda kafin a shawo kan lamarin, har an kashe mutane hudu. Shi ma kuma wanda aka kai asibitin, ya cika a hannun masu kiwon lafiya, saboda rauninsa.

Kakakin hukumar 'yansanda na yankin, DSP Bala Elkana, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce hukumarsu ta shawo kan lamarin, jama'a sun hankalta, amma yace bashi da tabbacin rahoton rasuwarr na asibitin. Ya kara da cewa, mutun hudu ne suka riga mu gidan gaskiya. Haka zalika, ya ce suna bin diddigin lamarin, kuma sun chafke mutum uku da ake zargi da kisa rigimar tun usuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel